'Yan Sanda sun kama 'hatsabibin mai garkuwa da mutane' kan kisar tsohon jami'in dan sanda
- 'Yan sanda a Jihar Imo ta kama wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Deberechi Chukwu kan halaka wani jami’in ‘yan sanda mai murabus a garin Mgbala da ke karamar hukumar Oguta
- Mike Abattem, Jami’in hulda da jama’an yan sandan Jihar Imo ya ce an kama wanda ake zargin yayin da yake yunkurin tserewa daga jihar zuwa wata mai makwabtaka da ita
- Ana zargin Chukwu yana cikin ‘yan gidan yarin da suka balle gidan gyaran halin Owerri sannan yana cikin wadanda suka dinga halaka jami’an tsaron jihar
Imo - Rundunar ‘yan sandan Jihar Imo sun kama wani Deberechi Chukwu bisa zarginsa da halaka tsohon jami’in ‘yan sanda a yankin Mgbala da ke karamar hukumar Oguta a jihar, The Cable ta ruwaito.
Mike Abattem, jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar Imo, ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da yake yunkurin tserewa daga jihar.
Kakakin rundunar ya ce Chukwu yana daya daga cikin ‘yan gidan yarin da suka balle gidan gyaran halin Imo inda yace ya hada kai wurin kashe-kashen jami’an tsaro a jihar.
Kakakin ya ce yana daya daga cikin wadanda suka addabi yankin da garkuwa da mutane
Kamar yadda The Cable ta bayyana, kakakin ya ce:
“Bayan ofishin ‘yan sanda na Agwa ya samu bayanai kan kisan da ya auku a ranar 1 ga watan Fabrairun 2022 da misalin karfe 9:52 na dare na wasu matasa da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne a garin Mgbala da ke karamar hukumar Oguta a Jihar Imo wadanda suka hada kai wurin halaka wani tsohon jami’in ‘yan sanda, Christain Kpatuma wanda mazaunin Mgbala ne bayan sunyi garkuwa da shi sannan suka halaka shi a wani daji tare da jefar da gawarsa a harabar gidansa.”
Rudunar ta ce ta kama wani Deberechi Chukwu akan kisan tsohon dan sandan a garin Mgbala da ke karamar hukumar Oguta a Jihar Imo.
Mike Abattem, kakakin ‘yan sandan Imo ya ce an kama wanda ake zargin yana kokarin tserewa wata jihar.
Bayan samun bayanai ne kwamishinan ‘yan sandan Jihar, CP Rabiu Hussaini ya yi saurin tura rundunar ‘yan sanda zuwa anguwar Agwa inda suka yi ram da wadanda ake zargin ya yi aika-aikar.
Chukwu ya bayyana hanyoyin kamo sauran ‘yan kungiyar sa
Yayin bincike ne aka gano cewa Deberechi Chukwu yana cikin masu garkuwa da mutanen da suka addabi jihar kuma yana cikin wadanda suka balle gidan yarin Owerri da ke Jihar Imo.
Wanda ake zargin ya horar da yara wadanda suka addabi garin Agwa. Kuma akwai rahotanni da dama a wurin jami’an tsaro na kashe-kashen da suka yi.
Ya yi bayanai sosai akan yadda za a kamo sauran mambobin kungiyar tasa wadanda yanzu haka ake nema ido rufe a cewar kakakin.
Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur
A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.
Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.
An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng