An Gurfanar Da Ɗan Shekara 21 Kan Lakaɗa Wa Sufetan Ƴan Sanda Duka Da Sace Masa N80,000

An Gurfanar Da Ɗan Shekara 21 Kan Lakaɗa Wa Sufetan Ƴan Sanda Duka Da Sace Masa N80,000

  • An gurfanar da wani Stephen Monday dan shekara 21 kan yi wa dan sanda mai mukamin sufeta duka tare da yi masa sata a Legas
  • Masu shigar da kara sun shaida wa kotu cewa Monday da wasu mutanen sun lakada wa Sufeta Folorunsho duka a Ebute Meta suka kuma sace masa N80,000 da hulansa
  • Mrs F.F. George, alkaliyar kotun ta bada belin Monday ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Fabrairun 2022

Jihar Legas - An gurfanar da wani mutum dan shekara 21, Stephen Monday, a gaban kotun Majistare ta Ebute Meta a Jihar Legas kan zarginsa da duka da sata.

The Punch ta rahoto cewa wanda aka yi karar ya yi wa wani dan sanda, Sufeta Folorunsho Lawal, duk ne yayin da dan sandan ke aikinsa a unguwar Otto, Ebute Meta.

Kara karanta wannan

An kashe ma'aikaciyar FIRS ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis a Legas

An gurfanar da ɗan shekara 21 kan lakaɗa wa Sufetan ɗan sanda duka da sace masa N80,000
An gurfanar da wani mutum kan lakaɗa wa Sufetan ɗan sanda duka da sace masa N80,000. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

An zargi Monday da yaga unifom din Lawal cikin tuhume-tuhume uku na duka, sata da aikata abin da ka iya tada rikici a gari, rahoton The Punch.

An karanto masa rahoton kamar haka:

"Kai, Stephen Monday, da wasu da ake nema, a ranar 29 ga watan Janairun 2022, misalin karfe 03.30 na yama, a G-Express, Otto, Ebute Meta, a Legas, kun ci zalin wani Sufeta Folorunsho Lawal ta hanyar dukansa da yaga masa unifom wanda hakan laifi ne a karkashin sashi na 173 na dokar masu laifi na 2015 ta Jihar Legas.
"Kai, Stephen Monday, da wasu da ake nema, a ranar da lokacin da aka ambata a farko, a kotun nan, kun aikata abin da ka iya tada zaune tsaye ta hanyar kai wa Sufeta Lawal hari yayin da ya ke aikinsa da doka ta halasta masa, hakan laifi ne a karkashin sashi na 168 (d) na dokar masu laifi na Jihar Legas ta 2015.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

"Kai, Stephen Monday, da wasu da ake nema, a ranar da lokacin da aka ambata a farko, a kotun nan, sun sace N80,000 da hula beret da kudinta ya kai N20,000 mallakar Sufeta Lawal, hakan laifi ne a karkashin sashi na 287 na dokar masu laifi na Jihar Legas ta 2015".

Alkaliyar kotun, Mrs F.F. George, ta bada wanda ake zargin a hannun beli sannan ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Fabrairun 2022.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164