Bayan 'yan kwanaki, an kama mutum 4 kan zargin ƙona gonar Obasanjo da gangan

Bayan 'yan kwanaki, an kama mutum 4 kan zargin ƙona gonar Obasanjo da gangan

  • Hukumomin tsaro sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu wurin cinna wuta a gonar OLusegun Obasanjo da ke Jihar Benue
  • Hakan na zuwa ne kimanin kwanaki shida bayan afkuwar gobarar da jami'an tsaro suka yi zargin da gangan aka cinna wutan suka kuma sha alwashin kamo wadanda suka aikata
  • Bayan afkuwar gobarar, tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ya nuna takaicinsa game da lamarin sai dai ya gode wa Allah babu wanda ya rasa ransa

Jihar Benue - An kama mutane hudu kan zarginsu da cinna wuta a gonar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ke Jihar Benue, Channels Television ta ruwaito.

Gonar tana yankin Howe ne a karamar hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Benue a wani katafaren fili inda ake noma mangwaro na lambu da wasu kayayyakin abinci masu yawa.

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

Bayan 'yan kwanaki, an kama mutane 4 da suka banka wa gonar Obasanjo wuta a Benue
An kama mutum 4 kan zargin cinna wuta a gonar Obasanjo. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kama su ne kwanaki bayan cinna wuta a gonar mai girman hecta 2,420. A cikin wata sanarwa, Kehinde Akinyemi, Mai magana da yawun tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Bayan afkuwar lamarin, mahukunta a Jihar ciki har da gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom sun sha alwashin binciko wadanda suka tafka barnar domin a hukunta su, rahoton Channels Television.

"An gano cewa da gangan aka cinna wutan, dole a hukunta wadanda suka aikata laifin," a cewar Gwamna Samuel Ortom kamar yadda sakataren watsa labaransa, Nathaniel Ikyur ya bayyana.

A bangarensa, tsohon shugaban kasar ya mika godiya ga dukkan mutanen da suka kira shi suka masa jaje bisa afkuwar lamarin, yana mai farin cikin cewa ba a rasa rai ba.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta

Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta

Tunda farko, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi alawadai kan kona gonarsa da wasu batagari suka yi a garin Howe da ke Karamar Hukumar Gwer ta Kudu a Jihar Binuwai a kwanakin karshen makon nan, The Punch ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasar mai shekaru 84 ya kwatanta lamarin a matsayin mummunan abu kuma ya ce sai jami’an tsaro sun gano wadanda suka tafka ta’asar.

The Punch ta ruwaito yadda batagari suka babbake gonar Orchard wacce mallakin babban mutumin ne na Hilltop da ke Abeokuta a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164