Zaben 2023: Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga tsaka mai wuya
- Yayinda masu niyyar takara a zaben shugaban kasa a 2023 suka fara bayyana niyyarsa, har yanzu ba'a ji daga wajen Sanata Rabiu Kwankwaso ba
- Kwankwaso ne yazo na biyu a zaben fidda gwanin APC a shekarar 2014, bayan shugaba Muhammadu Buhari
- A 2019 kuwa, ya sake takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP
Kano - Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya shiga tsaka mai wuya kan yadda siyasar 2023 zata kasance.
Majiyoyi masu karfi sun bayyana cewa tsohon dan takaran kujeran shugaban kasan zai bayyana ra'ayinsa game da 2023 nan ba da dadewa ba.
Daily Trust ta ce wani babban jigon Kwankwasiyya ya bayyana mata cewa Kwankwaso na shawarar samar da wata sabuwar tafiya gabanin zaben 2023.
Yace:
"Na san nan da karshen wata ko a farkon Maris, shi (Kwankwaso) da wasu shahrarrun yan siyasa na shirin samar da wata tafiya, amma ba jam'iyya ba,"
Ya ce wasu yan siyasa irinsu Buba Galadima da Suleiman Hunkuyi na bada shawarar samar da sabuwar jam'iyya amma Kwankwaso bai goyon bayan haka.
Ya kara da cewa:
"Ya nada ra'ayin sabuwar jam'iyya ba za tayi karko ba kuma da wuya a samu yin rijista kafin 2023. Saboda haka ake son kafa wata tafiya da za'ayi amfani wajen tattaunawa cikin wata jam'iyya mai ci."
Yan bangaren Osinbajo sun tuntubi Kwankwaso
Hakazalika an tattaro cewa wasu yan bangaren mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sun tuntubi Kwakwaso, duk da cewa Osinbajo bai bayyana niyyarsa ba tukun.
Wata majiya mai karfi tace har Shugaban jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya yi kira ga Kwankwaso ya koma APC.
A cewar majiyar:
"Tattaunawa na gudana tsakanin Oga da su. Suna son ya dawo APC amma ana shawara kai. Ba a yanke ba."
Mutanen Twitter sun ba PDP shawarar ta tsaida Peter Obi/Kwankwaso a zaben 2023
A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta bibiya abin da mutane suke fada a shafin sada zumunta na Twitter a ranar Laraba, 2 ga watan Fubrairu 2022.
Kevin Odanz ya jawo gardama da ya ce Peter Obi ba zai kai labari idan ya nemi tikitin PDP ba, ya ce ko zai yi nasara, 'Yan Arewa ba za su zabe shi ba.
Tuni wasu suka shiga maida masa martani, su na cewa tsohon gwamnan na Anambra ne zai iya doke APC, musamman idan ya tafi da Kwankwaso
Wani Otumba ya ce ya fahimci siyasar Najeriya, ya gano cin zabe sai an hada da yankin Arewa, ya na ganin Kwankwaso zai taimaka wajen doke APC.
Asali: Legit.ng