Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun afka wa mutune a kan titi gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro a Jihar Kaduna
  • Sakakamon harin, rayyuka shida sun salwanta yayin da wasu suka jikkata kamar yadda ganau suka bayyana
  • Mai magana da yawun yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, bai amsa kirar da aka masa ba don jin ba'asi

Kaduna - Wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta baiwa iyalan yan sanda bakwai da aka kashe milyan 7

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a hanya a Kaduna, sun kashe shida
Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Ya kara da cewa:

"Yanzu jami'an tsaro suna kwashe daliban makarantar zuwa wani wuri mai tsaro."

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, bai amsa kirar da aka masa ba yayin hada wannan rahoton.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164