Ci gaba: Bayan sikari, fulawa, gishiri da siminti, Dangote ya fara harhada motoci

Ci gaba: Bayan sikari, fulawa, gishiri da siminti, Dangote ya fara harhada motoci

  • Attajirin dan kasuwar Najeriya, Aliko Dangote tare da hadin gwiwar jihohin Kano, Kaduna da kamfanin Stellantis Group sun fara aikin hada motoci
  • Kamfanin ya fara aiki gadan-gadan a cikin watan Fabrairu kuma yana da damar hada motoci kusan 120 a kowace rana a kamfanin
  • Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce, za ta yi amfani da sabbin fasahohi da tsarukan tsaro yayin da take kokarin sake kulla alaka da dillalai a fadin kasar

Hamshakin attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote tare da kamfanin Peugeot mallakin Stellantis, gwamnatocin Kano da Kaduna, sun fara aikin hada motoci a Najeriya.

Ana sa ran za su fara fafatawa da kamfanin Innoson Motors, wani kamfani da ya shahara a yankin Kudu wajen wannan harka.

Dangote ya fara hada motoci
Ci gaba: Bayan sikari, fulawa, gishiri da siminti, Dangote ya fara harhada motoci | Hoto: businessday.ng
Asali: Getty Images

Kamfanonin dai na hada motocin ne a sabon kamfanin Greenfield Ultima Assembly da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

An gina kamfanin ne don yin aiki da cikakken iko kuma ana kyautata zaton zai iya harhada motoci kusan 120 a kowace rana.

Meye kamfanin yace?

Daraktan kira a masana’antar, Ibrahim Issa Gachi ya bayyana cewa, sabbin motocin da za a ke hadawa za su yi amfani da na’urorin zamani na fasaha da kuma na tsaro da za su tabbatar da tsaron masu amfani dasu, kamar yadda Legit.ng ta samo.

Sanarwar ta Gachi ta kuma ce, kamfanin ya tabbatar da cewa kayayyakin hada dukkan sabbin motocin da za a hada za a yi su ne daga kasuwannin cikin gida.

Har ila yau, don inganta siyar da sabbin samfuran Peugeot, su Dangote na hada hulda da dillalan Peugeot a duk fadin kasar don tabbatar da karbuwa a kasuwa da kuma tabbatar da cewa kamfanin ya sami ingantaccen suna.

Kara karanta wannan

Buhari ya bada izinin fitar da N115.4 billion don fadada titin Kano-Kazaure-Kongwalam

Yadda kamfanin ya fara

A 2016, gwamnatin jihar Kaduna, da kamfanin Dangote da kuma Bankin masana'antu ne ke da rinjaye a hannun jarin mota kirar Peugeot dake Kaduna da ta lalace.

A 2017, rahotanni sun bayyana cewa hamshakin dan kasuwar, Dangote ya samu lasisin kafa kamfanin Peugeot a Najeriya shekaru biyar da suka wuce.

A wani labarin, kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a baya-bayan nan, karin 30% na farashin hannun jarin simintin Dangote wanda ya biyo bayan karuwar gine-ginen a Najeriya daga 'yan kasa da gwamnati ya ba da gudummawa ga karin dukiyarsa.

Legit.ng a bincikenta, ta kawo muku wasu sabbin abubuwa guda 4 masu ban sha'awa game da hamshakin attajirin wanda a halin yanzu dukiyarsa ta kai dala biliyan 13.9.

Karuwar arzikin da Dangote ya samu ya sa attajirin zai iya kashe dala miliyan 1 (N415m) a kullum nan da shekaru 40 masu zuwa.

Kara karanta wannan

Karshen Korona: Jirgi zai fara jigila daga Dubai zuwa Najeriya ranar 5 ga wata

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.