Gwamnatin Zamfara ta baiwa iyalan yan sanda bakwai da aka kashe milyan 7

Gwamnatin Zamfara ta baiwa iyalan yan sanda bakwai da aka kashe milyan 7

  • Gwamnatin Zamfara ta bada kyautan kudi ga iyalan jami'an yan sanda bakwai da yan bindiga suka kashe
  • Yan bindiga sun tare yan sanda a hanya suka hallakasu kuma kuma bankawa motarsu wuta
  • Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Arewa maso yamma dake fuskantar annobar yan bindiga

Gusau - Gwamnatin jihar Zamfara ta baiwa iyalan jami'an yan sanda bakwai da yan bindiga suka kashe a jihar kudi N7 million.

A baya kun ji yadda yan bindiga suka kaiwa jami'an yan sanda harin kwantan bauna a hanyar Tofa-Magami, ranar 8 ga Nuwamba, 2021.

Kwamishanan yan sandan jihar, Ayuba Elkana, ya baiwa iyalan kowanne cikin kudi milyan guda-guda madadin gwamnatin jihar, rahoton ChannelsTV.

Gwamnatin Zamfara ta baiwa iyalan yan sanda bakwai da aka kashe milyan 7
Gwamnatin Zamfara ta baiwa iyalan yan sanda bakwai da aka kashe milyan 7
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

Elkana yace gwamnatin ta basu kudin ne don rage radadi da halin da suka shiga sakamakon rashin mazajensu.

Ya yi bayanin cewa jami'an yan sanda sun sadaukar da kawunansu don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

A cewarsa, yan sandan da abin ya shafa sune Jonah Markus, Solomon Abiri, Stephen Ishaya, Nura Ibrahim, Abdul Garba, Musa Lawal da Zubairu Sadiq.

Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

A wani labarin kuwa, yan bindiga masu garkuwa da mutane kimanin 200, sun dira garin Yangayya dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina cikin daren Alhamis, 3 ga watan Junairu, 2022.

Premium Times ta ruwaito cewa yan bindiga sun kashe Dagacin garin tare da mutum hudu.

Wani mazaunin Jibia, Halilu Kabir, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun kwashe sa'o'i uku suna cin karensu ba babbaka.

Yace:

"Sun shigo kan babura kuma suka fara harbi. Yayinda suke bi gida-gida suka kashe mutum hudu da suke kokarin guduwa."

Kara karanta wannan

Za'a shirya Fim na musamman kan Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng