Yadda 'yan sandan Najeriya suka tatsi N1m daga dalibi bayan daura masa bindiga a kai

Yadda 'yan sandan Najeriya suka tatsi N1m daga dalibi bayan daura masa bindiga a kai

  • Wani dalibin Najeriya mai suna Clement Ehinomen ya sanar da yadda jami'an 'yan sanda suka tatsi kudi har N1 miliyan daga wurin shi
  • Ya sanar da cewa, lamarin ya faru ranar Asabar inda 'yan sanda suka kama shi da dan uwan shi tare da garkame su a wani ofishin 'yan sanda
  • Sun bukaci ya kira 'yan uwansa da abokan arziki wadanda suka tara masa sama da miliyan daya, 'yan sandan sun sa shi ya fitar kuma ya basu

Benin, Edo - Wani dalibin Najeriya ya bayyana yadda wasu 'yan sanda suka saka masa bindiga a kai kuma suka tatsi kudi har naira milyan daya daga wurinsa.

Lamarin ya faru ne wurin karfe 1 na yammacin ranar Asabar a Benin da ke jihar Edo, yankin kudu kudu na Najeriya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Dalibin mai suna Clement Ehinomen ya sanar da Premium Times a ranar Litinin cewa, kusan jami'an 'yan sanda hudu ne suka yi amfani da motarsu wurin tare motarsa kirar Mercedes Benz GLK a tsakiyar titi kuma suka tirsasa shi da dan uwansa fitowa.

Yadda 'yan sandan Najeriya suka tsati N1m daga dalibi bayan daura masa bindiga a kai
Yadda 'yan sandan Najeriya suka tsati N1m daga dalibi bayan daura masa bindiga a kai. Hoto daga thecable.ng
Asali: Facebook

Dukkan jami'an suna dauke da bindigogi kuma suna saita shi da ita, Ehinomen mai shekaru 24 ya sanar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a yi wa motar fenti da kalar 'yan sanda ba kuma jami'an ba sanye suke da kayan 'yan sanda ba, hakan ne yasa Ehinomen ya rude ya gaza tantancewa 'yan sanda ne ko 'yan fashi.

"Suna sanye ne da bakar riga mai karamin hannu da wando. Na ji tsoro kwarai kuma har kuka na yi. Suna aiki tamkar 'yan fashi da makami," yace.
“Bana busa komai kuma bana shan komai, ba tukin ganganci nake yi ba. Sun tambaye ni lasisin tuki na da takardun mota ta, duk na ba su. Sun duba motar tare da duba safayar taya, sun ga komai cas."

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

Bayan kammala duba motar kuma sun ga babu komai na laifi, jami'an 'yan sanda sun kwashi Ehinomen da dan uwansa, wanda ba shi da isassar lafiya zuwa wani ofishin 'yan sanda a wajen Benin inda suka kulle su.

Ehinomen ya ce 'yan sandan sun tirsasa shi ya kira abokai da 'yan uwan sa wadanda suka tura masa kudi asusun bankin sa wanda daga bisani ya cire kuma ya basu

"Sun ce in fara kiran mutane da za su ba ni N7 miliyan ko kuma baza su bar ni ba," Ehinomen ya ce.

Ya ce 'yan sandan sun ki yadda ya tura musu kudin, sai suka je aka cire su. Sai wurin karfe takwas na dare suka sake mu.

Cike da damuwa dalibin ya je Twitter ya wallafa labarin sa, lamarin da ya janyo hankalin jama'a da kungiyoyi, ciki har da Segun Awosanya, mai rajin kare hakkin dan Adam wanda aka fi sani da Segalink.

Kara karanta wannan

Ahmed Musa ya wallafa sako mai ratsa zuciya bayan fitar Najeriya daga AFCON

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, Bello Katongs, a ranar Talata ya tabbatar wa da Premium Times aukuwar lamarin amma ya ce suna son tabbatar da 'yan sanda ne ko a'a.

An biya shi kudin shi

A ranar Litinin, Ehinomen ya wallafa wani hoto a shafinsa na Twitter inda ya ke nuna wasu makuden kudi a kan tebur.

"Mun gode wa Ubangiji, an dawo min da kudi na kuma an cafke jami'an 'yan sandan. Na gansu," ya rubuta.

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Najeriya ta halaka wasu mutum 23 da ake zargin 'yan ta'adda ne, inda suka sake kama yan bindiga guda 37 a kananan hukumomi uku da ke jihar Sokoto.

Yayin zantawa da manema labarai ranar Litinin a Sakkwoto, mataimakin Sifeta Janar, Ahmad Zaki, ya bayyana yadda aka kama wadanda ake zargin da bindiga kirar AK-47 guda 32, makamai masu linzami guda 2, harsasai sama da carbi 1,000 da mugayen makamai.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Yaro mai shekara 13 ya soka wa matashi mai shekara 19 wuka a Borno

Ya ce an gano hakan ne lokacin da 'yan sanda suke gudanar da aiki na musamman domin yaki da ta'addanci wanda su ka yi wa lakabi da "Operation Sahara Storm".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng