Masha Allah: NUC ta amince wa BUK ta fara yin digiri a fannin Shari'ar Musulunci

Masha Allah: NUC ta amince wa BUK ta fara yin digiri a fannin Shari'ar Musulunci

  • Hukumar Kula da Jami'o'i ta Najeriya, NUC, ta bawa Jami'ar Bayero da ke Kano izinin fara yin digiri a Shari'ar Musulunci, B.A. Shari'a
  • Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito a shafin intanet na hukumar JAMB a ranar 31 g watan Janairun shekarar 2022
  • Har wa yau, Hukumar ta NUC ta amince da fara yin wasu sabbin kwasa-kwasan digiri na hadin gwiwa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Kano da Minna

Jihar Kano - Hukumar Kula da Jami'o'i ta Najeriya, NUC, ta amince a fara gudanar da karatun digiri a bangaren shari'ar musulunci a Jami'ar Bayero da ke Kano, BUK, rahoton The Cable.

Hukumar ta kuma amince da wasu kwasa-kwasai 11 a tsangayar ilimi wato education.

Shari'a na daga cikin ginshikin addinin musulunci.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya aikawa Majalisa sunayen sababbin mukaman da ya nada a Gwamnati

Masha Allah: NUC ta amince wa BUK fara yin digiri a fanin Shari'ar Musulunci
Jami'ar BUK za a fara yin digiri a fannin Shari'ar Musulunci. Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukunce-hukuncen shari'a sun samo asali ne musamman daga Al-Kurani mai girma, hadisan manzon Allah (SAW).

JAMB ta sanar da amincewar cikin sanarwar da ta fitar a ranar 31 ga watan Janairu a shafinta na intanet.

A cewar sanarwar, an amince Jami'ar BUK ta fara Digiri na Shari'a wato B.A. Shari'a.

An kuma amince da fara wasu kwasa-kwasai a Kwallejin Ilimi

Ita kuma Kwallejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano, an amince mata fara wasu kwasa-kwasai na hadin gwiwa guda uku.

Su ne B.A. (Ed.) Islamic Studies; B.Sc. (Ed.) Biology Education da B.Sc (Ed.) Chemistry Education.

Ita kuma Kwallejin Ilmi ta Minna, kwasa-kwasan hadin gwiwa da aka amince mata ta fara sun kunshi B.A. (Ed.) History Education, B.A. (Ed.) Hausa Education da B.A. (Ed.) Arabic Education, B.A. (Ed.) Islamic Studies.

Kara karanta wannan

Jerin fitattun ciniki 12 da aka yi zuwa ranar karshen cefanen 'Yan wasa a Turai a 2021/22

Saura sun hada da B.Sc. (Ed.) Biology Education, B.Sc.(Ed.) Mathematics Education and B.Ed. Social Studies da B.A. (Ed.) English Education.

A baya-bayan nan hukumar ta amince da kafa wasu karin jami'o'i biyu a Jihar Legas.

Borno: Zulum zai wajbata rubuta NECO a dukkan makarantun jiharsa

A wani labarin, Farfesa Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Borno ya yi alkawarin yin iyakar iyawarsa wurin mayar da jarabawar NECO dole ga makarantun jiharsa, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce yana sa ran hakan zai tabbata bisa yakinin shugaban hukumar jarabawar NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi zai amince da wajabta jarabawar ga duk makarantun gwamnatin jihar.

Farfesa Zulum ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Usman Jidda Shuwa, wanda ya gabatar da wannan bukatar yayin da ya kai ziyara ga Farfesa Wushishi a Maiduguri a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164