Babu wani abu mai suna 'tubabben dan bindiga', kawai a kasheshu: El-Rufa'i

Babu wani abu mai suna 'tubabben dan bindiga', kawai a kasheshu: El-Rufa'i

  • Gwamna Nasir El-Rufa'i ya jaddada cewa babu ruwansa da maganar yafewa yan bindiga masu garkuwa da mutane
  • Gwamnan ya dade yana kira ga hallaka duk dan bindigan dake daji kuma babu maganar sulhu
  • A 2021, an hallaka sama da mutum duba daya a jihar Kaduna a shekarar 2021

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, a ranar Talata ya yi watsi da shirin da gwamnatin tarayya ke yi na yafewa yan bindigan da suka mika wuya da sunan tuba.

El-Rufa'i yace shi dai gwamnatinsa basu yarda da wani abu da suna 'tubabben dan bindiga' ba.

A cewarsa, babu wata gwamnati da zata cigaba indai ana zaman sulhu da yan ta'adda masu addaban jama'a.

El-Rufa'i
Babu wani abu da suna 'tubabben dan bindiga', kawai a kasheshu: El-Rufa'i Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wani dan shekara 69 ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin karban rahoton adadin mutanen da aka sace da wadanda kashe a shekarar 2021.

Yace duk wanda ya dauki bindiga kuma ya yiwa yan Najeriya barazana bai cancanci afuwa ba, kawai a kashe shi.

A cewarsa:

"Zaman lafiya na da muhimmanci, duk da koma bayan da aka samu. Zamu cigaba da jaddada cewa bamu yarda da wani abu da suna tubabben dan bindiga ba."

‘Yan bindiga sun aika mutane 1, 192 barzahu, sun dauke 3, 348 cikin shekara 1 a Kaduna

Akalla mutane 1, 192 suka mutu a hannun ‘yan bindiga, sannan kuma an yi garkuwa da wasu mutum 3, 348 a jihar Kaduna a shekarar da ta wuce.

Wannan bayani yana cikin rahoton harkar tsaro da aka fitar daga watan Junairu zuwa Disamban 2021 wanda kwamishinan tsaron cikin gida ya gabatar dazu.

Mista Samuel Aruwan ya gabatar da wannan rahoto ne ga Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a ranar Talata, 1 ga watan Fubrairu 2022.

Samuel Aruwan ya ce an samu mutuwar mutane 720 a yankin tsakiyar Kaduna a sakamakon garkuwa da mutane, rikicin kabilanci, da sauran tashin-tashina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng