Na kashe mutane sama da 20 amma yanzu na tuba, Yaron Turji da aka damke
- Jami'an yan sandan Najeriya sun cika hannu da daya daga cikin dan ta'adda Bello Turji a jihar Katsina
- Matashin dan shekara 21 ya bayyana adadin mutanen da ya kashe a baya amma yanzu ya koma ga Allah
- Hukumar yan sandan ta bayyana cewa tana cigaba da bincike kuma zata gurfanar da shi
Funtua - Naziru Sani, daya daga cikin yaron dan bindiga Bello Turji, ya bayyana adadin mutanen da ya kashe a hare-haren da suka kai amma yanzu ya tuba bayan shiga hannu.
Dan ta'addan ya bayyana hakan yayin hira da manema da Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya shirya a hedkwatar hukumar ranar Talata, rahoton Vanguard.
Naziru, wanda dan asalin garin Tsafe ne a jihar Zamfara ya shiga hannu ne a karamar hukumar Funtua, jihar Katsina, SP Gambo ya bayyana.
Naziru yace:
"Da ni aka kai hare-hare karkashin umurnin maigidana Turji, kuma na kashe mutum 20 a baya amma na tuba yanzu."
"Na gudu daga dajin Jangebe a Zamfara inda Turji yake kai hare-hare yanzu. Na gamu da yan sanda a Funtua, yayinda nike kokarin zuwa Suleja a jihar Neja inda iyaye na suke.Na bar matata da yarana a garin Makera, Tsafe jihar Zamfara."
Kudin da Turji ke biyan yaransa
Yayinda aka tambayesa adadin yaran da Bello Turji ke da su kuma nawa yake biyan yaransa, Naziru yace:
"Muna da yawa. Ban san takamammen adadin ba amma akwai daruruwa kuma ina samun tsakanin N20,000 da N30,000 bayan kowani hari."
Kakakin yan sanda, SP Gambo Isah, ya bayyanawa yan jarida cewa:
"Bisa da labaran leken asiri, hukumar ta samu nasarar damke Naziru Sani dan garin Makera, karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, wani dan ta'adda da ya addabi Katsina da kewaye."
Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, an kama wani likita da ake zargin ya yi jinyar harbin bindiga ga dan ta'adda Bello Turji a jihar Sokoto.
An kama likitan mai suna Abubakar Kamarawa ne a wani gagarumin samame da jami’an tsaro suka kai kan 'yan ta'addan.
An kama shi ne tare da wasu 'yan ta'addan a wasu ayyuka daban-daban a fadin kananan hukumomi uku na jihar Sokoto.
Kananan hukumomin sun hada da, Illela, Rabah da Goronyo, duk a yankin gabashin Sokoto.
Asali: Legit.ng