An kashe ma'aikaciyar FIRS ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis a Legas

An kashe ma'aikaciyar FIRS ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis a Legas

  • Wasu miyagun yan bindiga da a yanzu ba a san ko su wanene ba sun halaka wata ma'aikaciyar FIRS a Jihar Legas
  • Maharan sun kashe Mrs Ibironke Oluremi Adefila ne a safiyar ranar Asabar a lokacin da ta ke hanyar zuwa aiki a Legas
  • Yan sanda sun tabbaar da afkuwar lamarin inda suka ce matar ta cika tun kafin a kai ta asibiti kuma yanzu an fara bincike

Jihar Legas - Wasu yan bindiga a karshen makon da ta gabata sun kashe babbar ma'aikaciya a Hukumar Tattara Haraji na Kasa, FIRS, mai suna Mrs Ibironke Oluremi Adefila.

Daily Trust ta rahoto cewa maharan da ake zargin makasa ne sun halaka marigayiyan ne a gidan ta da ke Ikorodu a Legas.

An gano cewa sun rika bin sahun ta ne a lokacin da ta ke hanyar ta na zuwa wurin aiki a safiyar ranar Juma'a, 28 ga watan Janairun 2022.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

An kashe ma'aikaciyar FIRS ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis a Legas
Legas: An kashe ma'aikaciyar FIRS a hanyar zuwa aiki a ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis. Hoto: LIB
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta ce maharan sun kashe Adefila ne a unguwar Powerline da ke Laketu, Ikorodu da ke kallon Awalu Group of Schools.

An ce marigayiyan ta ce ga garin ku kafin ta iya karasawa asibiti.

Ganau ya magantu

Wani da abin ya faru a idonsa amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya jiyo daya daga cikin maharan na cewa, 'ita ce; ita ce' nan take suka far mata da adduna da gatari da wukake, Vangaurd ta ruwaito.

Alaba Jobi, wani dan uwan marigyiyan ya koka yana mai cewa, "Abin da ya kara bamu tsoro shine cewa a ranar an shirya taro don bikin karin girma da ta samu a ofis."
"Wani abin mamaki shine ba a sace komai ba kuma babu sassan jikinta da aka taba."

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Yan sanda sun tabbatar da mutuwar ta, sun fara bincike

Yan sanda sun ce bayanai game da matar a asibiti ya nuna cewa ta mutu tun kafin wasu mutane da ke wucewa suka tsince ta suka kai ta asibitin.

Kakakin yan sandan Jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kara da cewa a halin yanzu jami'an suna bin sahun makasan.

Ya ce Kwamishinan Yan Sanda ya bada umurnin a mika binciken zuwa sashin binciken kisa da ke SCID, Panti, Yaba.

Ya kuma tabbatarwa iyalan wacce ta rasu cewa za a binciko wadanda suka kashe ta sannan a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164