Kasar Sin ta hana mu bashi, yanzu Turai zamu je nema: Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kasar Sin ta daina bata bashin kudi don cigaba da wasu ayyuka
- Ministan Sufuri ya ce yanzu Gwamnatin Buhari ta garzaya kasashen Turai don samun basussukan kudi
- Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tn na gida da na waje
Abuja - Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa dalilin da yasa aka gaza kammala wasu ayyukan layin dogo rashin kudi ne daga wajen gwamnatin kasar Sin.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara yunkurin neman yadda zata samu bashi daga wajen kasashen Turai tunda kasar Sin ta rike kudinta.
Ya bayyana cewa idan aka samu nasarar samun kudi daga wajen Turai, za'a kammala ayyukan, rahoton SR.
Amaechi yace:
"Mun gaza cigaba da manyan ayyuka da yawa saboda rashin kudi. Yan kasar Sin sun daina bamu kudi. Yanzu mun fara nema a wajen Turai."
"Amma idan naga irin kudaden da wasu kasashe ke karba idan aka kwatanta da wanda Najeriya ke karba, sai in yi mamakin babatun da yan Najeriya ke yi."
Amaechi yace za'a cigaba da aiki kan Abuja-Itakpe. Yace da tuni an kammala aikin amma an samu sabani ne da dan kwangilan.
Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tn
Ofishin Manejin basussukan Najeriya DMO ta bayyana cewa kawo karshen Satumban shekarar nan ta 2021, ana bin Najeriya bashin N38.005tn.
Wannan na kunshe cikin jawabin da DMO ta saki a shafinta na yanar gizo ranar Talata.
Jawabin yace:
"Bisa al'ada, Ofishin Manejin basussukan Najeriya DMO ta wallafa jimillar basussukan da ake bin Najriya kawo 30 ga Satumba, 2021."
"Wannan ya hada da basussukan gida da na waje, jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya."
"Bashin ya zauna a N38.005tn ko $92.626bn kawo karshen rubu'i na 3 na shekarar 2021."
Asali: Legit.ng