Maganar kashe Hanifa ta shiga majalisar wakilai, an caccaka tsinke kan nema mata adalci
- Majalisar wakilai ta tatauna batun kisan Hanifa Abubakar da malaminta ya yi a jihar Kano
- Majalisar ta kuma nemi a gudanar da bincike yadda ya kamata domin a kama duk wanda ke da hannu a cikin lamarin
- Ta kuma bukaci a gaggauta yin adalci da hukunta su don hakan ya zama izina ga sauran mutanen da ke da irin wannan manufar
Majalisar wakilai ta yi kira ga hukumomin da suka dace da su tabbatar da ganin cewa an yi bincike a kan lamarin kisan Hanifa Abubakar sosai kuma cikin hikima don kamo duk wanda ke da hannu a lamarin.
Majalisar ta kuma ce ya kamata a gaggauta yin adalcin da ya kamata a lamarin ta yadda hukuncin zai zama izina ga masu irin wannan kudirin.
Majalisar ta yi kiran ne yayin da take nazari kan kudirin da Hon. Kabiru Idris ya gabatar kan lamarin a zauren majalisar.
Idan za kun tuna, Abdulmalik Mohammad Tanko, malamin Hanifa mai shekaru 5 wacce ta kasance dalibar makarantar Nobel Kids a Kwanar Dakata, ya yi garkuwa da ita a ranar 4 ga watan Disambar 2021, sannan ya nemi a biya kudin fansa.
Sai dai kuma ya kashe ta bayan ya karbi kudin fansa.
A kudirin nasa, Idris ya ce:
"Ina fatan jan hankalin wannan gida mai martaba zuwa ga wani abun bakin ciki da ya afku a jihar Kano a ranar 20 ga watan Janairun 2022.
"Jami'an tsaro da suka hada da na yan sandan Najeriya da rundunar tsaro ta farin kaya sun kama wani Abdulmalik Tanko da wasu mutane biyu wadanda suka yi garkuwa da kashe wata yarinya yar shekara biyar Hanifa Abubakar, dalibar makarantar Noble Kids a Kwanar Dakata da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.
"Malamin Hanifa, Abdulmalik Mohammad Tanko ya yi garkuwa da ita a ranar 4 ga watan Disamba 2021 inda ya bukaci a biya kudin fansa N6,000,000.
"Ya karbi wannan kudi amma sai da ya kashe ta, lamarin da ya sanya mutanen jihar Kano da kasar baki daya cikin kaduwa.
"Mai girma kakakin majalisa, wanda ya kamata ya kare yarinya karama da ke a karkashin kulawarsa shine ya sace ta sannan ya kashe ta.
“Akwai bukatar mu duba wannan lamarin domin irin wadannan abubuwan suna kara bayyana kalubalen tsaro da al’ummarmu ke fuskanta. Wannan abun kunya ne da damuwa ace yaran makaranta suna cikin rashin tsaro, sannan ana sacewa da kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba."
Da take amincewa da kudirin, majalisar ta yabawa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da jami’an tsaro kan yadda suka yi taka-tsantsan wajen gudanar da ayyuka da kuma tabbatar da adalci.
Majalisar ta kuma bukaci wanda ya gabatar da kudirin da ya shirya tawaga da za ta kai ziyara tare da jajantawa iyayan marigayiyar da daukacin al’ummar jihar Kano.
Ta umurci kwamitocin ta akan Adalci da 'Yancin Dan Adam da su tabbatar da bin wannan kuduri.
Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi
A baya mun ji cewa Ministan ilimi na kasa, Mallam Adamu Adamu ya jinjinawa gwamnatin jihar Kano kan matakan da ta dauka domin magance lamarin mutuwar Hanifa Abubakar, yar shekaru 5 da malaminta ya kashe ta.
Adamu wanda ya yi magana ta hannun daraktan labarai kuma jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Mista Ben Goong, a Abuja, ya yi Allah wadai da kisan Hanifa da malaminta, Abdulmalik Tanko ya yi bayan ya sace ta.
Ministan ya kuma ce yana sanya idanu sosai kan ci gaban domin tabbatar da ganin cewa an hukunta wanda ake zargin, Pulse.ng ta rahoto.
Asali: Legit.ng