Ohworode na masarautar Olomu: Abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Ohworode na masarautar Olomu: Abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Ga duk wanda ya san asalin Najeriya har zuwa yanzu ya san cewa Ohworode din masarautar Olumu, Richard Layieguen, Ovie Ogoni-Oghoro bai kasance basaraken da ya fi kowanne dadewa a kujerar sarauta ba a Najeriya, sai dai ya kasance abin alfahari a tarihin shugabancin gargajiyar Najeriya.

Sarakunan da ke karkashin sa sun taba kai karar basaraken mai shekaru 105 saboda kin cin naman yanka da ya yi.

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105
Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Baya ga wannan da sauran matsalolin da ya fuskanta yayin da ya ke kan karagar mulki, masarautar Olomu wacce Richard ya ke shugabanci ta kasance masarauta mai tarihin zaman lafiya a Jihar Delta.

Legit.ng ta gabatar da abubuwa 5 muhimmai dangane da basaraken da ya fi kowanne tsufa a kan karagar mulki.

1. Sirrin tsawon rayuwarsa

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har a wannan lokacin da Najeriya ta shiga cikin matsatsi kamar yadda Macro Trends ta ruwaito, Ohworode na masaratar Olomu ya ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali duk da shekarun sa 105.

A wata tattaunawa da The Punch ta yi da shi dangane da rayuwar sa, ya ce duk nufin Ubangiji ne wanda ya ci gaba da ba shi lafiya da tsawon shekaru.

Richard ya ce a rayuwar sa bai taba bayar da shaidar karya ba, lalata da matan mutane, zalunci ko kuma zaluntar wani.

Ya kara da cewa ba ya shan giya ko sigari sannan ya na zama cikin tsaftataccen wuri ne.

Shi ne auta a cikin ‘yan uwansa 21 kuma ya na tunanin sun yi gado ne na tsawon rai.

2. Mabiyin addinin kirista ne

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsalolin tsaro, Buhari ya ba da tabbaci

Basaraken ya bayyana yadda ba ya cin naman yanka don sadaukarwa da sauran abubuwa na tsafe-tsafe don sam bai yarda da hakan ba.

Ya bayyana yadda a shekarar 1989 ya ki amincewa da naman saniyar da aka yanka don wasu harkoki na gargajiya, wanda hakan yasa sarakunan da ke karkashin sa suka kai shi kotu suna bukatar a cire shi daga mulki saboda kin bin harkokin gargajiya.

3. Rayuwar auren sa

Ya fara tuka mota a shekaraer 1974 kuma ya yi auren sa na fari a 1949 wanda ya haifi yara 8. Ya sake aure bayan matar sa ta farko ta rabu da shi inda ya haifi yara 4 da ita.

Duk yaran sa yanzu haka sun kammala karatun su.

4. Abubuwan da basaraken ya fi son yi a rayuwarsa

Abubuwa 3 yafi son yi a rayuwar sa, zagaya lambu, karatu da kuma yawon bude ido.

Kasancewar shekarun sa sun yi nisa, ya daina harkar lambu sai dai ya na karatu babu kakkautawa.

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

Legit.ng tattaro bayanai a kan yadda ya kasance mutum mai ilimin gaske hakan yasa Olu din Warri, Ogiame Atuwatse III yayin da ya kai masa ziyara ya kira Richard da “kogin ilimi”.

5. Ya ziyarci ko wacce nahiya da ke duniya

Ba abin mamaki bane idan aka ce basaraken ya kai ziyara ko wacce nahiya kuma har yanzu ya na son yawo. Ya sanar da The Punch hakan yayin da ta tattauna da shi a 2017.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng