Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

An zargi wasu daga cikin mambobin IPOB da hallaka wani makiyayi a kwanan nan yayin da al'amarin ya jefa iyalansa, uban gidan sa dan kabilar Ibo da wadanda suka san shi cikin alhini.

Makiyayin, Muhammad Alarabe alias Ogbodo, ya kai kimanin shekaru 20 ya na kula da shanu, dan kabilar Ibo kafin harbe shi da aka yi a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu, 2022.

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindiga shanu 30
Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindiga shanu 30. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Hakazalika, maharan sun sheke wasu daga cikin shanun uban gidan Alarabe, Chief Oeter Chukwuani Onyeabor, fitaccen mai sayar da shanu a jihar Enugu, wanda ya gaji kasuwancin daga marigayin mahaifinsa.

Iyalan Onyeabor sun yi fice a kasuwancin shanu sama da shekaru 200.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Duk da Onyeaobr ya siffanta maharan a matsayin "yan bindiga", al'amarin ya na nuna cewa mambobin ESN ne, yan awaren IPOB wadanda suka saba kai hari ga makiyaya a kudu maso gabacin kasar.

Wasu mazauna yankin sun ce ba dole a ce hakan ya shafi jan kunnen da IPOB suka yi ba, inda suka yi gargadi a kan siya da siyar da naman shanu a kudu maso gaba.

Takardar da ke sanar da jan kunnan an alakanta ta ne ga mai magana da yawun IPOB, Emma Powerful.

Sai dai har yanzu, yan sanda ba su kama kowa a kan harin ba. Kakakin rundunar yan sandan jihar, ASP Daniel Ndukwe, har yanzu bai samu cikakken bayani a kan al'amarin ba amma akwai sa ran zai fitar da takarda.

Sai dai abun takaici, wasu sun yi murna game da kisan Alarabe a kafafan sada zumuntar zamani.

A satin da ya gabata, wani bidiyo da ya yi yawo a kafafan sada zumunta ya bayyana Alarabe face-face cikin jini da matattun shanu da wasu cikin radadi saboda irin tarin harsasan da aka harbe su da su.

Kara karanta wannan

An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta

Duk da an jiyo muryar wasu suna jajanta al'amarin, amma babu wanda ya ambaci inda al'amarin ya auku, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Domin tabbatar da gaskiyar al'amarin, Daily Trust ta je yankin Akwuke a kudancin karamar hukumar Enugu inda ake yada jita-jitan al'amarin ya auku.

Yayin cigaba da bincike, har zuwa Ugbowka a Nkanu da ke gabashin gundumar jihar Enugu, inda Onyeabor, mai shekaru 62 ya bada labarin yadda al'amarin ya auku.

"An kai harin misalin karfe 5:25 na yamma. Lokacin ina zaune a baranda muna magana da wasu kwastomomi da suka zo siyan shanaye a wannan ranar.
"Ina siyar da shanaye na a nan ne. Ba na kai su kasuwa. Mutane ke zuwa daga nesa da kusa su siya a wuri na. Wannan shi ne sana'ar iyalina na tsawon shekaru.
"Yayin da muke hira da masu siyan shanayen, na kawo musu goro don tarbar su, ba mu dade muna hira ba muka fara jin harbe-harbe a iska ba kakkautawa a gaban farfajiyar gidajen mu, daga babban titi.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

"Na yi yunkurin fita in ga abunda ke faruwa, sai dai mata ta ce ta dakatar da ni, inda take shaida mini cewa yan bindiga ne suke harbe shanayen mu kada in yi kuskuren fita.Har kwastomomi na sun ja kunne a kan kada in fita waje.
"Kafin kiftawar ido, 'yan bindigan sun sheke shanaye 22. A cikin shanayen da suka sheke akwai wadanda muke sayarwa naira 700,000 duk guda daya saboda tsabaragen girman su.
"Akwai shanayen da suka fada daji da raunukan harsasai, inda aka gan su daga baya a daji. Takwas daga cikin wadanda suka samu raunukan sun mutu daga baya. Dan uwa na, tabbas kaddara ta auko mini," a cewarsa.

Onyeabor ya bayyana yadda ba da jimawa da aukuwar al'amarin yan bindigan, SPA gwamna Ifeanyi Ugwuanyi, ya kira jami'an tsaro inda suka zo duba gurin da ta'addancin ya auku.

Ya ce hadin gwuiwar sojoji daga bangare na 82 na Sojojin Najeriya da ke jihar Enugu su ne na farkon ziyartar gurin.

Kara karanta wannan

Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

Jami'an hadin gwuiwan tsaron sun gabatar da taro daga baya a fadar sa a Ibeagwa-Nike inda aka yanke shawarar rubuta wasika ga gwamnatin jihar game da mummunan al'amarin da ya auku.

"Washe garin ranar, 20 ga watan Janairu, DSS suka taho tare da jami'an hukumar 'yan sanda. Sun zanta da ni kuma na fada musu yadda al'amarin ya auku. Inda suka ce za su dau mataki akai,"a cewar shi.

Onyeabor ya tuna lokacin da a shekarar 2013, barayin shanu suka auka karamar makiyaya ta a cikin farfajiyar iyalina suka yi awon gaba da shanaye 35.

Niger: Rayuka birjik sun salwanta, gidaje sun babbake a sabon harin ƴan ta'adda

A wani labari na daban, mutane da dama sun halaka sakamakon farmakin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Galkogo da ke karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Yayin tattaunawa da The Cable dangane da mummunan harin, Jibrin Alawa, shugaban kungiyar matasa ta jihar, ya ce harin ya auku ne da misalin karfe 3 na rana har zuwa 6 na yammacin ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

Alawa ya ce kusan mahara 200 ne suka afka har kauyen a baburan su rike da miyagun makamai suna harbi ko ta ina. A cewarsa, maharan sun banka wa gidaje da dama wuta sannan sun kone sansanin ‘Yan Sa Kai da ke kauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng