Yan fashi sun fara shiga aikin yan sanda, Shugaban hukumar jin dadin yan sanda ya koka

Yan fashi sun fara shiga aikin yan sanda, Shugaban hukumar jin dadin yan sanda ya koka

Hukumar jin dadin yan sanda, PSC, ta bayyana takaicin yadda barayi da yan fashi ke samun shiga aikin dan sanda a Najeriya.

Shugaban hukumar, Musliu Smith, ya bayyana takaicinsa ne a taron wayar da kai na kwana daya kan daukan sabbin ma'aikata a Birnin Kebbi, ranar Litinin.

A cewarsa, wannan babban kalubale ne kuma ya zama wajibi a san yadda za'a magance shi.

Musliu Smith ta samu wakilcin, mataimakin diraktan hukumar, Hawa Komo.

Yace:

"Daya daga cikin kalubalen da hukumar ke fuskanta lokacin daukan sabbin jami'ai a 2019 shine rashin ilimin wadanda suka cika fom wanda abin takaici ne."
"Wajibi ne mu kwadaitar da yaran kwarai su rika neman aikin dan sanda."

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

"Idan kimtsattsun matasanmu sun ki shiga aikin dan sanda, a ina zamu samu yan sandan kwarai?"
"Mun ga lokacin da barayi yan fashi suka shiga neman aikin dan sanda.. Wajibi ne mu hada kai wajen tabbatar da cewa mutanen kwarai ake dauka aiki."

Asali: Legit.ng

Online view pixel