Yanzu-Yanzu: Fitaccen sarki a Arewacin Najeriya, Isma'il Ari II ya riga mu gidan gaskiya
- Labari daga majiyoyi sun bayyana cewa, mai martaba Sarkin Moriki ta jihar Zamfara ya kwanta dama
- Sarkin ya rasu ne a jihar Kaduna bayan jinya na wani lokaci kamar yadda rahotanni suka bayyana
- Za a yi jana'izar marigayi mai martaba Isma'il Muhammad a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara
Zurmi, Jihar Zamfara - Gidan talabijin na TVC ya rahoto cewa, Sarkin Moriki, Mai Martaba Sarki Isma’il Muhammad Ari II ya riga mu gidan gaskiya.
Sarkin ya rasu ne a wata cibiyar lafiya dake Kaduna bayan ya sha fama da rashin lafiya na wani lokaci.
Sarkin Moriki na Masarautar Moriki ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar (2 maza 3 mata) da kuma dangi da dama, kamar yadda Radio Nigeria ta ruwaito.
Za a yi jana'izar shi a yau Talata da karfe 3 na rana a fadar sarkin da ke Moriki a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sarki mai daraja ta daya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki
A wani labarin, Sarkin Lafiagi, Alhaji Saadu Kawu Haliru ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun ce basaraken ya rasu ne a wani asibiti a Abuja misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Alhamis.
Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa za a kai gawarsa jihar Kwara a ranar Juma'a zuwa Lafiagi, ƙaramar hukumar Edu inda za a yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.
Marigayi Sarkin Lafiagi, sarki ne mai sanda mai daraja ta ɗaya wanda ya hau mulki a 1975 kuma ya yi bikin cika shekaru 45 kan mulki a ranar 21 ga watan Oktoban 2020.
Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara
Asali: Legit.ng