Da dumi-dumi: Tsohon sanatan Najeriya ya yi babban rashi na mahaifiyarsa
- Mahaifiyar tsohon dan majalisar dattawa wanda ya wakilci yankin Bayelsa ta gabas, Ben Murray-Bruce, ta kwanta dama
- Sanata Bruce ya bayyana cewa mahaifiyar tasa ta amsa kiran mahaliccinta ne a safiyar yau Talata, 1 ga watan Fabrairu
- Ya kuma yi wasu zantuka masu taba zuciya a kan rashin babban bangon nasa, inda ya ce ya yi kewarta matuka
Tsohon sanata wanda ya wakilci yankin Bayelsa ta gabas, Ben Murray-Bruce, ya sanar da labarin mutuwar mahaifiyarsa, Madam Margaret Murray Bruce.
A cewar tsohon dan majalisar, mahaifiyar tasa ta mutu ne da misalin karfe 4:40 na safiyar Talata, 1 ga watan Janairu.
Da yake bayyana hakan a Facebook, Sanatan ya ce ya samu saukin bakin cikin da yake ciki kasancewar ya san cewa ya baiwa mahaifiyar tasa dukkan kulawar da zai iya bata a rayuwarta.
Ben Bruce ya rubuta:
“Shakka babu rayuwa tamkar yashi ne a iska, yau tana nan, gobe ta tafi. Mahaifiyata ta tafi. Ta mutu da misalin karfe 4:40 na safiyar yau. Babbar tsanin rayuwata, babbar aminiya ta, komai nawa - ta tafi.
“Saukin bakin cikina shine cewa a lokacin da take da rai, ba abunda kudi zai iya siya da banyi mata ba, abu mafi muhimmanci, na kasance tare da ita, na bata lokacina, na bata komai nawa.
“A lokuta masu yawa, zan je gidanta na rungume ta sannan nayi wasa da ita ba tare da wani dalili ba illa saboda kauna, irin na ‘da da uwa. Ina kaunarki, mahaifiyata, kuma ina kewarki. Hakan akwai radadi sosai. Ni naki ne har abada.”
Bana so na daurawa kowa nauyi: Dattijo ya gina kabarinsa, ya siya duk abun da za a sha a yayin bikin mutuwarsa
A wani labarin na daban, mun ji cewa wani dattijo mai shekaru 70, Leo, ya haka kabarinsa a yayin da yake shirye-shiryen mutuwarsa. Mutumin ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda talakawan garinsa na shiga halin matsi don binne mutanen da suka mutu a baya-bayan nan.
A wani bidiyo da Afrimax ta wallafa, mutumin ya bayyana cewa baya so ya zama jidali ga mutane bayan ya mutu.
Domin cimma wannan manufa, mutumin ya haka kabarinsa, ya shirya komai da za a yi amfani da shi a yayin bikin mutuwarsa.
Asali: Legit.ng