Innalillahi: Mummunar gobara ta lamushe gonar Obasanjo ta Benue

Innalillahi: Mummunar gobara ta lamushe gonar Obasanjo ta Benue

  • Gagarumar gobara ta lamushe gonar tsohon shugaban kasa Najeriya, Olusegun Obasanjo, wacce ke jihar Benue
  • Mummunan ibtila'in ya fada wa gonar ne a ranakun karshen mako kamar yadda mai kula da ita, Zubello Muhammad ya sanar
  • An yi kokarin kashe gobarar amma abun ya ci tura, sai da ta lashe bangare mai girma kuma har yanzu ba a san tushen wutar ba

Benue - Gobara ta lashe gonar lambun tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo a Howe da ke Karamar Hukumar Gwer a jihar Benue.

An samu labarin aukuwar mummunan al'amarin a ranakun karshen mako kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Innalillahi: Mummunar gobara ta lamushe gnar Obasanjo ta Benue
Innalillahi: Mummunar gobara ta lamushe gnar Obasanjo ta Benue. Hoto daga thenationonlinng.net
Asali: UGC

Mai kula da gonar, Zubello Muhammad, ya bayyana yadda gobarar ta auku lokacin da yayi tafiya wajen anguwar dan aiwatar da wani aiki.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ya ce ya samu labari a ranar Asabar misalin karfe 2:00 na rana cewa gonar ta kama da wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai kula da gonar ya bayyana yadda aka yi kokarin kashe wutar amma abun ya ci tura sai bayan ta lashe bangare mai girma na gonar.

Muhammad ya ce har yanzu ba a gano abunda ya haddasa al'amarin ba. Sai dai ya na zargin makiya ne suka haddasa gobarar.

A cewarsa, an girbe duk ciyayin da ke harabar gonar dan gudun sake aukuwar al'amarin.

Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni

A wani labari na daban, wata gagarumar gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Gamboru Ngala a jihar Borno, lamarin da yasa daruruwan 'yan gudun hijiran suka rasa matsuguni.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya auku da yammacin Lahadi inda gobarar ta lamushe wurare masu tarin yawa a sansanin.

Wani jami'in hukumar taimakon gaggawa ta jihar, SEMA, da ke Gamboru Ngala, Malam Yusuf Gulumba, ya sanar da Daily Trust cewa an fara binciken abinda ya kawo gobarar.

Ya ce mutanen da suka samu kananan raunika ba su da yawa, sun kuwa jigata ne yayin da suke kokarin kashe wutar duk da ba a rasa rai ko daya ba.

Gulumba ya yi kira ga gwamnatocin tarayya da na jihar da su samar da kayayyakin abinci da na bukata tare da matsuguni ga wadanda ibtila'in ya fada wa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng