Yanzu-Yanzu: Fusatattun Matasa sun mamaye kotun da ake shari'ar Ɗan Sarauniya a Kano
- Matasa sun mamaye kotun da ake shari'ar tsohon kwamishina, Muazu Magaji, sun nemi kotu ta yi wa Ɗan Sarauniya adalci
- A ɗaya ɓangaren kuma, Wata tawagar masu zanga-zangan sun ce suna neman a hukunta Ɗan Sarauniya, a yi wa Ganduje Adalci
- A halin yanzun, Alkalin kotun ya shaida wa Lauyoyin kowane ɓangare cewa ba zai cigaba da sauraron shari'ar ba sai matasan sun fita
Kano - Wasu matasa sun mamaye harabar kotun Majistire dake Nomansland, inda ake gudanar da shari'ar tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji (Ɗan Sarauniya).
Matasan ɗauke da Allunan rubutu suna faɗin, "A saki Muazu Magaji," yayin da suke neman a yi wa tsohon kwamishinan adalci, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Magaji wanda aka fi sani da 'Win Win' ko Ɗan Sarauniya,' an gurfanar da shi gaban mai shari'a Aminu Gabari, bisa tuhume-tuhume huɗu.
A takardar bayanan yan sanda ta farko, ana tuhumar Ɗan Sarauniya ne a a kan, ɓata sunan gwamna, da kalaman ƙarya masu hatsari da sauran su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A halin yanzun masu zanga-zangan sun tattaru a harabar kotun ɗauke da allunan rubutu, suna faɗin, "A saki Muazu Magaji, A saki Ɗan Sarauniya, Jagoran Win Win."
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangan ya ce:
"Ba mu zo nan dan mu tada yamutsi ba, mun zo ne mu nemarwa Jagora adalci. Muna son kotu ta yiwa jagoran mu, Muazu Magaji, adalci."
Magoya bayan Ganduje sun ɓarke da zanga-zanga
Kazalika, wata tawagar masu zanga-zangan, wanda suka bayyana kan su da ɗalibai, sun bukaci a yi wa gwamna Abdullahi Ganduje adalci.
A cewarsu, tsohon kwamishinan ya jima ya na zuga mutane kan gwamna Ganduje, kuma hakan na tayar da fitini tsakanin mutane.
Ɗaya ɗaga cikinsu, Aminu Muhammad, ya koka da cewa:
"Abun da muke bukata shi ne a yi wa gwamnan mu adalci, muna fatan (Ɗan Sarauniya) ya girbi abin da ya jima yana shuka wa,"
"Mai girma gwamna ya fi ƙarfin a yi wasa da shi, amma shi ya maida zagi da cin mutuncin gwamna kamar sana'arsa a Soshiyal Midiya."
Wane mataki kotu ta ɗauka?
A halin yanzun, Alkali ya shaida wa Lauyoyi cewa ba zai cigaba da sauraron shari'ar ba har sai masu zanga-zangan sun fice daga harabar kotu.
Lauyan Ɗan Sarauniya, Garzali Ahmad, ya roki masu zanga-zangan su bar harabar kotun, domin samun damar cigaba da zaman shari'a.
Lauyan yace:
"Alƙali ya shaida mana ba zai cigaba da sauraron ƙarar ba har sai dandazon mutanen sun fice. Wannan dalilin yasa nake haɗa ku da Allah ku bar nan wurin."
"Idan kuma ba haka ba, mutumin da kuke neman a yi wa adalci ba zai samu zuwa nan ba."
A wani labarin na daban kuma Rikici ya barke, mambobin jam'iyyar APC sun mamaye hedkwatar APC a Ekiti
Mambobin jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar Ekiti sun fara zanga-zangar nuna adawa da zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan jihar.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa APC ta shirya gudanar da zaɓen fitar da gwani ne a yau Alhamis, 27 ga watan Janairu, 2022.
Asali: Legit.ng