Duk ɗan bindigan da aka kama a tura shi ya haɗu da Allah, ita ce kaɗai mafita, Sarkin Katsina ya ɗau zafi

Duk ɗan bindigan da aka kama a tura shi ya haɗu da Allah, ita ce kaɗai mafita, Sarkin Katsina ya ɗau zafi

  • Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya bayyana cewa kashe duk ɗan bindigan da aka kama ne kaɗai hanyar kawo karshen su
  • Sarkin ya ce bai kamata a kama mutumin da ya kashe rayuka 20 zuwa 30 ba, kuma a tasa shi zuwa gidan gyaran hali
  • Ya kuma nuna farin cikinsa bisa ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda da gwamnatin tarayya ta yi

Katsina -Sarkin Katsina, HRH Abdulmumini Kabir, ya ce hanya ɗaya ta kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga ita ce duk wanda aka kama a kashe.

Vanguard ta rahoto cewa Sarkin ya yi wannan furucin ne a fadarsa dake Katsina, yayin da mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kai masa ziyara.

Yayin ziyarar, Osinbajo, ya shaida wa Sarkin cewa gwamnati ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta'adda, domin baiwa jami'an tsaro damar ɗaukan tsauraran matakai a kansu.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

Fadar Sarkin Katsina
Duk ɗan bindigan da aka kama a tura shi ya haɗu da Allah, ita ce kaɗai mafita, Sarkin Katsina ya ɗau zafi Hoto: Katsina Post FB Fage
Asali: Facebook

Yayin da yake martani kan haka, sarkin ya ce:

"Ina cikin damuwa, haka gwamna Masari, amma na yi matukar farin ciki a yanzu da aka ayyana su a matsayin yan ta'adda."
"Saboda haka yanzun zaku kama ku kashe, domin ita ce kaɗai mafita tun da shirin tattaunawar sulhu ya ci tura."

Me zai sa a kai ɗan bindiga gidan Yari?

Basaraken ya koka da cewa, "Ta ya mutum zai kashe rayuka 20 zuwa 30 amma a tura shi gidan gyaran hali? Ba zai haifar da ɗa mai ido ba, domin duk randa ya fito zai sake komawa ruwa ne."

Sarkin ya kuma yi kira ga mazauna jihar su koma ga Allah, su masa biyayya kamar yadda ya umarta, sannan su kyautata wa junan su.

Kara karanta wannan

Rayuwar Aure: Kotu ta datse Igiyoyin auren wata mata saboda mijin ya faɗa soyayya da kare

Kazalika ya bukaci Katsinawa su ƙaunaci junan su ta hanyar kokarin kare martabar junan su da riƙe wa juna sirri.

Mataimakin shugaban ƙasa ya kai ziyara jihar Kastsina ne domin jajantawa gwamnati da al'umma bisa rasuwar mahaifiyar Dahiru Mangal, Hajiya Murja Barau.

A wani labarin na daban kuma Cikin jihohi 36, An bayyana gwamnan jihar da ya fi kaunar zaman lafiya a Najeriya

Gidauniyar wanzar da zaman lafiya ta baiwa gwamnan jihar Enugu, lambar yabo ta gwamnan da ya fi son zaman lafiya a Najeriya.

Shugaban gidauniyar, Dakta Sulaiman Adejoh, yace sun yi nazari kan muhimman ayyukan gwamnan kafin su zaɓe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262