Bayan bankwana da 'yan uwa za a kai ta dakin miji, amarya ta fadi, ta rasu a take
- Allah mai iko da buwaya ya dauka ran amarya a ranar da za a kai ta dakin mijin ta a garin Damaturu da ke jihar Yobe
- Yusuph Baba Idi ya sanar da yadda amaryar ta gama bankwana da 'yan uwa da abokan arziki, amma sai ta zube a kofar gida
- Ya sanar da cewa an daura auren ta amma washegari za a kama hanyar Kano domin kai ta dakin mijin ta, sai rai ya yi halinsa
Allah mai yadda ya so, mai komai mai kowa, Ya dauki ran amarya washegarin da aka daura mata aure bayan ta gama sallama da bankwana da 'yan uwa da abokan arzikin ta.
Kamar yadda wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Yusuph Baba Idi ya wallafa, ya ce lamarin ya faru a garin Damaturu na jihar Yobe.

Kara karanta wannan
Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Asali: UGC
A cewar Baba Idi, 'yan uwan amaryar sun raka ta har kofar gida kuma za a kai ta Kano ne yayin da ta zube kasa, daga bisani rai ya yi halinsa.
Ya bukaci jama'a da a saka amaryar a addu'a kuma Allah ya yi mata gafara tare da saka mata da aljanna.
Kamar yadda wallafar ta ce:
"Daga Allah mu ke kuma gare shi za mu koma. Duniya abun tsoro! an daura auren wata baiwar Allah jiya a Damaturu.
"Yau 'yan uwan ta da abokan arziki sun rako ta kofar gida sun gama ban kwana a kan za a kai ta Kano, kawai ta zube kuma rai ya yi halin sa daga bisani.
"Ashe ban kwanan karshe suka yi gaba daya. Jama'a mu saka ta a addua. Mu na rokon Allah ya gafarta mata kuma ya saka mata da Aljanna.

Kara karanta wannan
Kano: Sadiya Haruna ta sha da kyar hannun Ƴan daba, sun yi yunƙurin watsa mata acid
"Dazu da safe na yi waya da 'yar uwar ta take fada min za su tafi Kano, kwatsam daga baya ta kira ni ta ce min amarya ta rasu."
Ango ya danƙara wa amarya saki a liyafar bikinsu kan waƙar da ta zaɓa a saka mata
A wani labari na daban, wasu ango da amarya sun kafa sabon tarihi na yin aure mafi gajarta a duniya.
Sun rabu ne a yayin da ake liyafar bikin su saboda wakar da amaryar ta zaba. A take kuwa angon ya dankara wa amaryar saki bayan rikicin da wakar ta janyo yayin da ake tsaka da shagalin bikin a Baghdad.
Kamar yadda aka tattaro, matar ta bukaci a saka mata wata wakar kasar Syria ne mai suna Mesaytara wacce Lamis Kan ya rera.
Asali: Legit.ng