Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda

Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda

Manyan jiga-jigan siyasa, yan kasuwa, attajirai, jami'an gwamnati, manyan jami'an yan sanda sun dira auren 'dan Sifeto Janar da hukumar yan sanda, IGP Alkali Usman, ranar Asabar, 29 ga Junairu, 2022.

A jawabin da Legit ta samu, an daura auren a fadar mai martaba Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi.

Daga bisani aka gudanar da walima a gidan gwamnatin jihar Borno inda Gwamna Babagana Umarar Zulum ya karbi bakuncinsu.

Daga cikin wadanda suka halarta akwai Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, Sanata Kashim Shettima; Ministan Sufurin jirgin sama, Hadi Sirika; karamin ministan mai, Timipre Sylva da Attajiri Alhaji Aliko Dangote.

Hakazalika akwai Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru; Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; da Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Ibrahim Na-idda, ya mutu

IGP na yan sanda
Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda Hoto: Tope Brown
Asali: Facebook

Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda
Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda Hoto: Tope Brown
Asali: Facebook

Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda
Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda Hoto: Tope Brown
Asali: Facebook

Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda
Dangote, Lawan, Jiga-jigan siyasa sun halarci auren 'dan gidan IGP na yan sanda Hoto: Tope Brown
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng