Gwamnatin tarayya na gina tituna 21 a jihar Kano, Minista Fashola

Gwamnatin tarayya na gina tituna 21 a jihar Kano, Minista Fashola

  • Babatunde Fashola ya ce gwamnatin APC ta yanzu na kira tituna tituna akalla guda 21 a cikin Kano da kewaye
  • Hakazalika a cewarsa, Gwamnatin Buhari ta kammala ginin gidaje domin rabawa mutane cikin farashi mai sauki
  • Ministan ya ce gwamnatin APC ta samu nasarori masu yawa fiye da gwamnatin Amurka dangane da ababen more rayuwa

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya na aiki kan titunan da jimmilan tsayinsu ya kai kilomita 960 guda 21 a jihar Kano.

Ministan ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kaiwa Gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje a Kano.

Diraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar aiki, Boade Akinola ya bayyana hakan a jawabin da ya saki, rahoton DailyTrust.

Kara karanta wannan

Ayiriri matasa: An rage farashin aure a Dawakin Tofa, jihar Kano

Fashola yace:

"A yanzu Gwamnatin tarayya na ayyukan tituna 21 a matsayin a Kano da kewaye kuma jimillan tsayinsu ya kai kilomita 960."
"Daga cikin wadanda suka shahara sune Titin Kano-Abuja, Kano-Katsina, Kano-Maiduguri, dss."

Minista Fashola
Gwamnatin tarayya na gina tituna 21 a jihar Kano, Minista Fashola Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Muna gina gidaje a Kano

Fashola ya kara da cewa Gwamnatin jihar ta kammala sashe na 1 da na 2 na shirin gina gidaje a jihar.

Ya kara da cewa Shugaban Buhari ya bada izinin mika gidajen ga jama'a.

Gwamna Ganduje ya jinjinawa Shugaba Buhari inda yace yana gab da mayar da jihar Kano cibiyar kasuwancin kasashen Afrika ta yamma.

Fashola: Buhari ya yi wa Gwamnatin Amurka fintinkau a ɓangaren yin ayyukan more rayuwa

A bangare guda, ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya ce gwamnatin jam’iyyar APC ta samu nasarori fiye da ta Amurka a bangaren yin ayyukan more rayuwa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

Mr Fashola ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis a Kano yayin wani taron tattaunawa na jam’iyyar APC.

An yi taron ne musamman don wayar da kan jama’a akan nasarorin da jam’iyyar ta samu cikin shekaru 7 da suka shude.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng