Ayiriri matasa: An rage farashin aure a Dawakin Tofa, jihar Kano
Yayinda matasa ke korafi kan tsadar aure a arewacin Najeriya, shugabanni a karamar hukumar Dawakin Tofa dake jihar Kano sun kayyade kudin da mai neman aure zai kashe.
DalaFM ta ruwaito cewa shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai ya tabbatar da hakan.
A cewarsa, daga yanzu babu saurayin da zai yi sake daukan dawainiyar wata budurwa, har sai ya fara tura magabatansa sun yi magana da iyayenta.
Kan lamarin kayan lefe kuwa, an takaice adadin kaya zuwa akwati uku kacal.
Majalisar karamar hukumar ta Dawakin Tofa, ta aiwatar da wannan sabuwar dokar ne biyo bayan shawarwari da ta yi da masarautar Bichi, wanda a karshe aka kafa kwamiti, na musamman domin tabbatar da dokar.
Jami’in hulda da jama’a na kananan hukumomin shiyar, Sagir Abdullahi Kwanar Huguma ya bayyana haka a jawabin da ya saki kuma manema labarai suka samu.
Asali: Legit.ng