Dan Sarauniya ya kurmance a kotu, ya tilasta Alkali dage zama

Dan Sarauniya ya kurmance a kotu, ya tilasta Alkali dage zama

  • Yan sanda sun kama Mu'azu Magaji, tsohon kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano a birnin tarayya Abuja
  • An garzaya da shi jihar Kano domin gurfanar da shi gaban kuliya kan zargin batawa iyalin Gwamna Ganduje suna
  • Yayin yunkurin kamashi da yan sanda sukayi, Magaji ya yi hadari kuma yace ya kurmance sakamakon haka

Kano - Tsohon kwamishanan ayyuka na jihar Kano, Muaz Magaji, wanda aka fi sani da 'Dan Sarauniya' ya kurmance a cikin kotu yayinda ake shirin gurfanar da shi ranar Juma'a.

A cewarsa, hakan ya faru sakamakon wani hadarin ya samu lokacin da yan sanda ke binsa a Abuja ranar Alhamis, rahoton DailyNigerian.

An damke Muazu Magaji ne ranar Alhamis a Abuja yayinda yake kokarin gudunma yan sandan dake binsa kuma yayi hadari sakamakon haka.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

Dan Sarauniya ya kurmance a kotu, ya tilasta Alkali dage zama
Dan Sarauniya ya kurmance a kotu, ya tilasta Alkali dage zama Hoto: DailyNigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayinda ya gurfana gaban Alkali Aminu Gabari ranar Juma'a, Lauyan Magaji, Garzali Ahmad, ya bayanawa kotu cewa ya kurmance sakamakon raunin da ya samu a hadari.

Lauyan ya kara da cewa sakamakon rashin jin magana, ba zai iya bada amsa kan tuhumar da ake masa ba.

Ya bukaci kotu ta bada belin Magaji domin ya tafi asibiti ganin Likita.

Alkali Gabari ya bada umurnin kai Muazu Magaji asibitin yan sanda kuma a tsareshi a can.

Ya dage zaman zuwa ranar Litinin, 31 ga Junairu. 2022.

Kama Dan Saurauniya

Wasu jami'an rundunar yan sandan Najeriya, a birnin tarayya Abuja sun kama Mu'azu Magaji, tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano.

BBC Hausa ta rahoto cewa lauyansa da iyalansa sun tabbatar da kama tsohon kwamishinan a daren ranar Alhamis, inda suka ce an kama shi ne yayin da ya ke hanyar komawa masaukinsa.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: 'Yan sanda sun cafke tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano, Mu'azu Magaji a Abuja

Barista Garzali Datti Ahmad, lauyansa ya fada wa BBC Hausa cewa suna zargin akwai hannun gwamnatin Jihar Kano a kamen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

iiq_pixel