Gwamnatin tarayya zata kara kudin mai bayan zaben 2023, Ministan Mai
- Karamin Ministan man feturin Najeriya yace dakatad da kara farashin mai da akayi ba na din-din-din bane
- Timipre Sylva yace tsawon watanni 18 kawai aka dakatar, daga nan zuwa bayan zaben 2023
- Yace wannan bai da alaka da zabe, kawai tausayi da jin kai ne irin na shugaba Muhammadu Buhari
Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Talata ta sanar da cewa an dakatad da cire tallafin man fetur na tsawon watanni goma sha takwas (18).
Hakan na nufin cewa za'a cire tallafin bayan zaben 2023.
Karamin Ministan arzikin man fetur, Timipre Sylva, ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa yayin hirar da masu magana da yawun shugaban kasa suka shirya.
Ya ce an dakatad da cire tallafin ne domin masu ruwa da tsaki su samu lokacin sake shirin daidaita yadda karin farashin mai, ba za'a tsananta halin da mutane ke ciki ba.
Sylva yace:
"Bamu da niyyar cire tallafin yanzu. Muna bada shawaran kara watanni 18 kuma mu bar yan majalisa suyi abinda suka ga ya dace."
Yayinda aka tambayesa shin hakan na da alaka da zaben 2023, Ministan yace:
"A'a, wannan kawai tausayin gwamnatin nan ne da shugaba Buhari. Yana son a shirya sosai kuma yace idan muna son cire tallafin, wajibi ne a kare mutuncin yan Najeriya."
NNPC ta bukaci a bata N3tr kudin tallafi: Ministar Kudi
Kamfanin man feturin Najeriya (NNPC) ta bukaci kudi N3 trillion daga wajen gwamnatin tarayya matsayin kudin tallafin man fetur na 2022 tun da an fasa kara farashin mai.
Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a fadar Shugaban kasa bayan zaman majalisar zartaswa FEC.
Ta bayyana cewa maimakon N470 billion da aka ware na kudin tallafin Junairu zuwa Yuni, yanzu za'a biya karin N2.557 trillion saboda farashin mai ya tashi a kasuwar duniya.
Asali: Legit.ng