Fasto ya rabo matar aure da 'ya'yanta mata 2 daga gidan miji, ya kawo su gidansa yana lalata da su a Ogun
- Fasto Timothy Oluwatimilehin mai kula da cocin kiristoci ta Spirit Filled International da ke Olomore a Abeokuta, yana hannun ‘yan sanda
- Hakan ya biyo bayan zargin sa da lalata da matar aure da kuma yaranta biyu bayan ya mara wa matar baya wurin barin gidan mijin ta
- Ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Ogun ce ta tallafa wa mijin matar wurin gano harkar banzar da ke aukuwa tsakanin su da gaggawar kai wa ‘yan sanda korafi
Ogun - Faston Cocin Spirit-Filled International da ke Olomore a Abeokuta, Timothy Oluwatimilehin yana hannun Rundunar ‘Yan sandan Jihar Ogun bisa zargin sa da yaudarar wata mata da yaranta biyu inda ya ke lalata dasu bayan zuga matar wurin barin gidan mijin ta, The Nation ta ruwaito.
Mijin matar, wanda ya kasa ceto matarsa da yaran nasa guda biyu daga hannun Fasto Oluwatimilehin akan lalatacciyar alakar da ke tsakanin su, ya samu taimakon ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Ogun, inda suka garzaya ofishin ‘yan sanda da ke Adatan don kai korafi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya sanar da manema labarai hakan a ranar Alhamis.
DSP Oyeyemi ya ce DPO din Ofishin ‘yan sanda na Adatan, SP Abiodun Salau, ya tura yaran sa don su kama faston.
Ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin ya amsa duk laifukan da ake zargin sa da aikatawa.
Kamar yadda Tribune ta ruwaito, Kakakin ya ce:
“Faston ya amsa laifukan inda ya bukaci a yafe masa. Yayi bayanin ya ce ya yi amfani da damar fadan da matar suka yi da mijinta wurin shiga tsakanin su don ya yi lalata da matar.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Lanre Bankole ya umarci jami’an yaki da satar mutane da bautar da kananun yara na bangaren binciken sirri don su ci gaba da bincike akan lamarin kuma suyi gaggawar gurfanar da mai laifin kotu.”
Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.
A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.
Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.
Asali: Legit.ng