Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kai hari Sakatariyar APC yayin da mambobi ke zanga-zanga a Ekiti
- An shiga tashin hankali a jihar Ekiti kan cece-kucen da yaƙi karewa wa game da zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC mai mulki
- Wasu tsageru sun fara harbe-harbe a babbar Sakatariyar APC yayin da mutane suka taru suna zanga-zanga
- Mambobin APC sun mamaye sakatariyar tun safe, inda suka nuna adawar su ga zaɓen wanda suke zargin an shirya maguɗi
Ekiti - Wasu fusatattun mambobin APC a jihar Ekiti sun mamaye Sakatariyar jam'iyya, inda suke zanga-zangar adawa da zaɓen fitar da ɗan takara, The Cable ta rauwaito.
APC mai mulkin jihar ta sanya yau Alhamis 27 ga watan Janairu, 2022 a matsayin ranar.da zata gudanar da zaɓen fitar da ɗan takarar gwamnan jihar.
Sai dai mambobin da suka tattaru a Sakatariyar sun zargi gwamnan jihar, Kayode Fayemi, da shirya maguɗi a zaɓen, inda suka ƙara da cewa ba za su shiga zaɓen ba.
An kai wa masu zanga-zanga hari
AIT ta rahoto cewa wasu da ake zargin yan bindiga ne sun farmaki masu zanga-zangan, waɗan da ke neman a ɗage zaben, a Sakatariyar APC dake Ekiti.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun fara gudun neman tsira yayin da harbe-harbe ya tsananta a cikin iska.
Wannan na zuwa ne bayan yan takara bakwai daga cikin masu muradin tikitin APC sun ayyana janye wa daga zaɓen saboda a ganin su ba'a shirya gaskiya ba.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa yan takarar sun bukaci jam'iyyar APC ta ƙasa da kuma ta jiha su gaggauta dakatar da zaɓen da aka shirya.
A cewarsu, hakan ne kaɗai zai magance abin da kan iya biyo baya na shiga shari'a kan zaɓen wanda ke baibaye da zarge-zarge da cece kuce.
A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari kan mutanen ƙauye, Sun halaka Manaja da yaronsa
Wasu yan ta'adda da ake zargin Fulani makiyaya ne sun halaka mutum biyu a wani sabon hari da suka kai ƙauyen jihar Ondo.
Yan bindigan sun buɗe wa Manajan gidan man Fetur da yaronsa ɗaya wuta, kuma dukka mutum biyun sun mutu.
Asali: Legit.ng