Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da wani katafaren kamfanin simintin BUA

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da wani katafaren kamfanin simintin BUA

  • Gabanin zarcewa zuwa jihar Zamfara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsaya a jihar Sokoto don gudanar da wasu ayyuka
  • Shugaban ya ziyarci wani katafaren kamfanin samar da siminti da aka yi jihar Sokoto, ya kaddamar da kamfanin
  • Kamfanin da Alhaji AbdulSamad Rabi'u ya samar an ce yana da karfin samar da tan miliyan uku na siminti

Jihar Sokoto - Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin simintin BUA mai karfin samar da tan miliyan uku a Sokoto da misalin karfe 12:20 na rana.

Shugaban ya samu rakiyar Gwamnan jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal; Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefele; Shugaban rukunin BUA, Alhaji AbdulSamad Rabi'u da shugaban kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da sauransu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Babban Sarki da gwamna ya tsige daga kujerarsa ya rigamu gidan gaskiya

An kaddamar kamfanin BUA
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da kamfanin simintin BUA a Zamfara | Hoto: dailytrust.com
Asali: Depositphotos

Jim kadan bayan kaddamar da kamfanin, shugaban kamfanin, Alhaji AbdulSamad Rabi’u, ya zagaya da shugaban kasar tare da tawagarsa.

Ana sa ran shugaba Buhari zai yi jawabi a wurin taron bayan takaitaccen rangadin da ya yi a sassan kamfanin.

Rahoton Channels Tv ya ce, Buhari kara da cewa a 1985 a matsayinsa na shugaban kasa a lokacin, ya zo Sokoto don kaddamar da aiki makamancin wannan.

Daga Sokoto, Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau

A wani labarin, TVCNews ta ruwaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fasa zuwa jihar Zamfara sakamakon bacin yanayi a sararin samaniya.

Shugaban kasan dai yanzu yana jihar Sokoto kuma zai koma birnin tarayya Abuja.

Buhari ya shirya kai ziyara wajen gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, don jajanta masa bisa rashin rayukan da akayi sakamakon hare-haren yan bindiga.

Kara karanta wannan

Buhari ya lula Zamfara domin jajantawa wadanda 'yan ta'adda suka yi wa barna

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.