Damfara: Jami'an EFCC sun yi ram da Michael Jackson a Legas

Damfara: Jami'an EFCC sun yi ram da Michael Jackson a Legas

  • Hukumar EFCC mai yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta kama wani Michaal Jackson a Legas da ake zargin dan damfara ne
  • An kama Jackson ne bayan hukumar EFCC ta samu bayanai na sirri da ke nuna cewa wasu mutane suna aikata damfara ta kwamfuta
  • Bayan kama Jackson, wanda ke basaja a matsayin, Ella, an kwato kayayyaki da dama da suka kunshi motocci, kwamfuta, wayoyin salula da sauransu

Jihar Legas - Jami'an hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arziki ta'annati, EFCC, sun kama wani da ake zargin mai damfara ne ta yanar gizo, Michael Jackson, kan zarginsa da damfara a Legas.

An kama wanda ake zargin ne a ranar Talata 25 ga watan Janairun 2022 bayan samun bayanan sirri da ke nuna wasu mutane suna aikata damfara ta hanyar amfani da kwamfuta, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar Valentine don yanke wa Hushpuppi hukunci a Amurka

Damfara: Jami'an EFCC sun yi ram da Michaal Jackson a Legas
Legas: EFCC ta kama wani Michaal Jackson da ake zargi da damfara. Hoto: Vanguard NG
Asali: Twitter

A cewar EFCC, Jackson, wanda ke gabatar da kansa a matsayin, Ella, namiji da ya koma mace ya damfari mutane miliyoyin naira.

An kama shi da motocci, kwamfuta da wasu kayayyaki

An kama wanda ake zargin, da ya yi ikirarin cewa yana sana'ar DJ, dauke da kayan tsibu da tsafi da ya yi ikirarin cewa suna taimaka masa wurin 'samun nasara'.

Vanguard ta rahoto cewa hukumar ta ce bayan kama wanda ake zargin, an kama wata Toyota 4 runner; Honda Accord daya da laptop kwamfuta biyu, MacBook daya da wani na'ura duk a hannunsa.

EFCC ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

Kara karanta wannan

Yadda jami'an EFCC suka je har kotu domin cafke wanda ake zargi a Legas

A wani labarin, hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta nemi taimakon 'yan Nigeria wurin neman wasu mutane hudu da ta ayyana nemansu ruwa a jallo kan damfara.

Hukumar a shafinta na Facebook, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba ta ayyana neman Akpodemaye Ikolo, Donald Olorunkoyede, Owootomo Tomilola Sunday, da Okuafiaka Bright Onyebuchi ruwa a jallo.

EFCC ta ce ana bincikar wadanda ake zargin ne kan laifuka masu alaka da damfara. Hukumar ta bukaci duk wani da ke da bayani mai amfani dangane da inda mutanen suke ya tuntubi ofisoshinta a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164