Abun Kunya: Mahaifi ya ɗirka wa diyarsa ta jini ciki saboda tsabar sha'awa

Abun Kunya: Mahaifi ya ɗirka wa diyarsa ta jini ciki saboda tsabar sha'awa

  • Yan sanda sun yi ram da wani mahaifi dan kimanin shekara 38 bisa zargin ɗirka wa ɗiyarsa ta jini juna biyu a jihar Bayelsa
  • Makotan mutumin sun bayyana cewa lamarin ya soma ne bayan mutuwar mahaifiyar yarinyar, inda ya maye gurbinta ta ɗiyarsa
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar ya tabbatar da cewa suna tsare da wanda ake zargi, ana cigaba da bincike

Bayelsa - Yan sanda sun kama wani ɗan shekara 38, Baridap Needman, a jihar Bayelsa bisa zargin ɗirka wa ɗiyar da ya haifa cikin shege.

Daily Trust ta rahoto cewa mutumin da ake zargin ya aikata wannan ɗanyen aiki ne a gidansa dake gefen hanyar PDP a babban birnin jihar, Yenagoa.

Jami'an tsaro sun kama mutumin, wanda ɗan asalin jihar Ribas ne, biyo bayan korafin da ƙungiyar (GRIT) ta shigar a kansa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa a Najeriya

Jihar Bayelsa
Abun Kunya: Mahaifi ya ɗirka wa diyarsa ta jini ciki saboda tsabar sha'awa Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Wasu makotan wanda ake zargi ne suka sanar da GRIT lokacin da suka gano yarinyar na ɗauke da juna biyu na tsawon watanni biyar, kuma mahaifinta ne ya mata cikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya fara cin zarafin ɗiyar tasa ne tun tana da shekara 7 a duniya, lokacin da yake sanya mata hannu a al'aura.

Ina mahifiyar yarinyar take?

Kazalika, lamarin ya ƙara muni bayan mutuwar uwar yarinyar shekaru kaɗan da suka gabata, kuma mahaifin ya maye gurbin matarsa da ɗiyar ta sa.

A cewar makotan su, yarinyar wacce ta ke JSS 3 a karamar Sakandire, tana kwana a gado ɗaya tare da mahaifinta, yayin da kaninta ke kwanciya a ƙasa.

Da farko sun kaiwa ƙungiyar kare haƙƙin 'ya'ya mata GRIT rahoto, wanda haka yasa jami'an yan sanda na caji ofis Ekeki suka damƙe mahaifin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanata ya sanar da kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Wane mataki za'a ɗauka?

Shugaban ƙungiyar GRIT, Dise Ogbise, ta ce zasu haɗa ƙarfi da ma'aikatar mata ta jihar Bayelsa wajen tallafa wa yarinyar har sanda Allah zai sauke ta.

Trubune ta rahoto Ta ce:

"Ba zamu zubar da cikin ba, yanzu haka mun damƙa yarinyar da kuma ƙaninta hannun iyalansu domin kula da su yadda ya dace. Zata kasance karkashin kulawar gwamnati."
"Ya kamata ta cigaba da zuwa makaranta, zamu ƙarfafa mata guiwa ta cika burinta na zama mawaƙiya."

Kakakin yan sanda reshen jihar, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da lamarin, yace wanda ake zargin na hannun SCID ta jiha domin gudanar da bincike.

A wani labarin na daban kuma Wata mata ta ɗauki cikin surukinta, ta haifi jikanta saboda ɗiyarta ta gaza samun juna biyu

Maree Arnold mai shekara 54 a duniya ta haifi diyarta ba tare da mahaifa ba, sakamakon haka ba ta iya ɗaukar juna biyu.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala: Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC

Matar ta kuma amince ta zama mahaifiyar kwayayen ɗiyarta da na mijinta, kuma ta haifi jikanta cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: