Yadda jami'an EFCC suka je har kotu domin cafke wanda ake zargi a Legas

Yadda jami'an EFCC suka je har kotu domin cafke wanda ake zargi a Legas

  • Jami'an hukumar EFCC sun dire a wata babbar kotun tarayya da ke Legas dauke da bindigogi inda suka dinga birkice ko ina suna neman wani
  • Sun bayyana wurin karfe 5 na yammacin Litinin kuma sun koma kotun da safiyar Talata duk a kokarin su na damke wani wanda ake zargi
  • Hukumar EFCC ta tabbatar da aikata hakan inda ta ce wani ta ke nema ta cafke domin kotun ta sake shi kuma an bukaci ya koma ranar Laraba domin cigaba da shari'ar sa

Legas - Jami'an hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, dauke da makamai sun kai samame tare da duba farfajiyar babbar kotun tarayya da ke Legas a kokarin su na damke wani wanda suke zargi.

Kara karanta wannan

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

Premium Times ta ruwaito cewa, jami'an hukumar sun zagaye farfajiyar kotun da ke yankin Waterside a Ikoyi ta jihar Legas.

"Jami'an EFCC dauke da bindigogi sun kai samamen farfajiyar babbar kotun tarayya wurin karfe 5 na yamma, bayan da yawa daga cikin ma'aikatan sun tashi daga aiki," wata majiya ta tabbatar.
Yadda jami'an EFCC suka je har kotu domin cafke wanda ake zargi a Legas
Yadda jami'an EFCC suka je har kotu domin cafke wanda ake zargi a Legas. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC
A yayin bayar da labarin yadda lamarin ya faru, wani ma'aikacin kotun wanda ya bukaci a boye sunan sa ya ce, "Jami'an EFCC sun iso kotun kuma suka dinga duba ginin kan abinda ba mu sani ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda wata majiya tace, "Shugaban kotun tarayya na Legas, A. O. Faji, wanda alkali ne ya sha mamaki yadda jami'an suka yi burus da tambayar da alkalin ya ke musu tare da cigaba da aikata abinda ya kai su.
"Mataimakin magatakarda, Christy Clement Ende, ya na ofis lokacin da suka yi wannan kutsen. Da safiyar Talata kuma suka sake zagaye farfajiyar kotun," majiyar tace.

Kara karanta wannan

Bidiyon matashin da ya hargitsa banki, ya kwace kadarar su kan kwashe masa kudi daga asusun sa

Abinda ya kai mu kotu, EFCC

EFCC ta tabbatar da wannan cigaban ga Premium Times a wani sakon kar ta kwana da ta aike mata a ranar Talata.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwujaren, ya yi bayanin cewa jami'an hukumar sun je kotun ne domin daukar wani wanda ake zargi mai suna Edrian Idida Osegie.

Uwujaren ya ce wanda ake zargin kotun ta bayar da umarnin sakin sa kuma za a sake gurfanar da shi ne a ranar Laraba.

Gurfanar da shi da za a sake yi ne yasa hukumar ta dauka wannan matakin, Uwujaren ya tabbatar.

Sai dai, ya musanta labarin da aka ce jami'an sun birkice ko ina na kotun domin su cafke wanda ake zargin.

Hukumar EFCC ta tuhumi Ahmed Kuru, manajan daraktan AMCON, kan zargin rashawa

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta na tuhumar Ahmad Kuru, Shugaban Hukumar Kula da Kadarori na Najeriya (AMCON), bisa zargin sa da laifin da ya shafi rashawa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

Wani babban ma'aikaci a hukumar yaki da rashawa ne ya tabbatar wa TheCable a ranar Laraba.

Ana zargin Kuru da yin sama da fadi da kuma saida wa makusanta kadarori a kan karyayyen farashi bayan an kwato daga hannun 'yan kasuwan da aka zarga da gaza biyan bashin da su ka ci daga bankuna, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng