Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban kwastam na Najeriya, Hamman Ahmad, ya rasu

Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban kwastam na Najeriya, Hamman Ahmad, ya rasu

  • Tsohon shugaban hukumar kwastam na kasa, Hamman Ahmad ya rasu a ranar Laraba yayin da yake da shekaru 78 da haihuwa
  • Dan uwan mamacin, Ibrahim Ahidjo ya tabbatar wa da manema labarai mutuwar tasa inda yace ya rasu ne a asibitin Abuja yayin da yake jinya
  • Mutuwar sa ta biyo bayan ta tsohon shugaban hukumar ne, Dikko Inde, wanda ya rasu a watan Fabrairun shekarar da ta gabata

FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar hana fasakwabri na kasa, kwastam, Hamman Ahmad, ya riga mu gidan gaskiya, rahoton Premium Times.

Ya rasu ne a ranar Laraba yana da shekaru 78 a duniya.

Yanzu-Yanzu: Tsohon shugaban kwastam, Hamman Ahmad, ya rasu
Tsohon shugaban kwastam, Hamman Ahmad ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Wani dan uwan marigayin, Ibrahim Ahidjo, ya tabbatarwa Premium Times rasuwarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin Gwamnan Ekiti na PDP: An fara baiwa hammata iska kan zargin murdiya

Ya ce Mr Ahmad ya rasu ne yayin da ake masa magani a wani asibiti a Abuja.

Rasuwarsa na zuwa ne bayan wani tsohon shugaban na kwastam, Dikko Inde, ya rasu a watan Fabrairu da ta gabata.

Ahidjo ya ce marigayi Ahmad dan asalin karamar hukumar Jada ne da ke jihar Adamawa kuma za a yi jana’izar sa ne a ranar Laraba a masallacin kasa da ke Abuja.

Ya rike kujerar shugaban hukumar lokacin mulkin Yar’adua

Mr Ahmad ya rike kujerar shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya ne daga shekarar 2008 zuwa 2009 a lokacin mulkin Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’Adua.

Shi ne ya gaji kujerar daga hannun Bernard Nwadialo kuma Jacob Buba ya gaje shi.

Kafin ya rike mukamin shugaban hukumar, shi ne mataimakin shugaban hukumar a hedkwatar ta da ke Abuja.

Marigayin ya yi karatun sa na firamare a makarantar firamare ta Jada daga shekarar 1956 zuwa 1963 daga nan ya zarce Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Ganye inda ya yi karatu daga 1965 zuwa 1969.

Kara karanta wannan

Najeriya ce ta 1 cikin jerin kasashen Afrika da ake amfani da man Bilicin, Sabon Bincike

Ya samu takardar shedar WAESC a Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Bauchi a shekarar 1970 sannan ya zarce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1977 inda ya yi digirinsa na farko.

Bayan ya yi hidimar kasar sa shekarar 1978 ya fara aiki da Hukumar Kwastam ta Kasa a matsayin Assistant Superintendent.

Ya yi ayyuka a rassan hukumar na daban-daban kamar; Valuation Unit, Hedkwatar Kwastam da kuma Tin Can Island inda daga nan ya samu karin girma ya zama mataimakin shugaban hukumar a 2005, sannan ya rike kujerar Jami'in sa ido a hedkwatar kwastam din har watan Mayun 2008 bayan nan ya zama shugaban hukumar.

Ya rasu ya bar matan sa biyu da yara

Ahmad ya rasu ya bar matan sa biyu da yara, jikoki da kuma kannin sa maza.

Cikin ‘yan uwansa akwai Usman Ahmad (Shehu Kojoli) wanda ya yi murabus daga shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Hali da Umar Ardo dan takarar gwamnan Jihar Adamawa kuma tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo shawarwari kan harkokin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta yi nasarar ƙwace kwallaben giya 1,906 a Jigawa

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164