Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Jonathan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Jonathan

  • Wasu ɗauke da bindugu da ake tsammanin masu garkuwa ne sun sace ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun yi awon gaba da, Jephthah Robert, a kofar gidansa dake kan hanyar Dimrose dake birnin Yanagoa
  • Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Bayelsa, ya tabbatar da cewa tuni suka fara aikin ceto mutumin da kama maharan

Bayelsa - Wasu miyagun yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun yi awon gaba da, Jephthah Robert, ɗan uwan tsohon shugabn ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan.

Jaridar Punch ta rahoto cewa maharan sun sace shi ne a kofar gidansa ranar Talata da misalin ƙarfe 9:30 na dare a kusa da hanyar Dimrose, Yenagoa, jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Mahaifi ya ɗirka wa diyarsa ta jini ciki saboda tsabar sha'awa

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Jonathan Hoto: channesltv.com
Asali: UGC

Shugaba kuma mamallakin kamfanin Zeetin Engineering Limited, Azibaola Robert, ƙani ne ga wanda yan bindiga suka sace kuma yan uwa ga Jonathan.

Shin yan sanda sun samu rahoto?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata gajeruwar sanarwa da ya fitar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto Butswat ya ce:

"Maharan sun ɗauke shi ne a kan hanyar Dimrose dake Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa. Tuni muka fara kokarin kubutar da shi da kuma kama masu garkuwan."
"A halin yanzun muna aiki tukuru kuma da alamun nasara a kokarin ceto shi."

An sako kwamishinan jihar Bayelsa

Garkuwa da ɗan uwan Jonathan na zuwa ne awanni 24 bayan kwamishinan cinikayya da kasuwanci na jihar Bayelsa, Federal Otokito, ya kuɓuta daga hannun yan bindiga.

Mahara sun sace kwamishinan ne ranar 20 ga watan Janairu, 2022 a cikin gidansa dake ƙauyen Otuokpoti, ƙaramar hukumar Ogbia, jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin Gwamnan Ekiti na PDP: An fara baiwa hammata iska kan zargin murdiya

Ya kwashe kwanaki biyar a sansanin waɗan da suka yi garkuwa da shi, kafin daga bisani su sako shi ranar Litinin.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

Wasu miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari na rashin imani ƙauyen Bobi, dake ƙaramar hukumar Mariga a jihar Neja.

Rahoton da The Nation ta tattara ya bayyana cewa maharan sun kashe dandazon mutane da har yanzun ba'a gano adadin su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262