Shugaba Buhari zai kai ziyara Jihar Zamfara ranar Alhamis

Shugaba Buhari zai kai ziyara Jihar Zamfara ranar Alhamis

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara Jihar Zamfara ranar Alhamis kamar yadda gwamna Bello Matawalle ya shaida
  • Gwamnan ya bayyana hakan ne a daren Talata a wani taro na gaggawa da ya yi da masu mukamai daban-daban a cikin gidan gwamnati
  • A cewarsa, Shugaban kasa zai kai ziyarar ne don yi wa mutanen karamar hukumar Anka da Bukkuyum jaje akan hare-haren da aka kai musu

Jihar Zamfara - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara Jihar Zamfara a ranar Alhamis mai zuwa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a wani taron gaggawa da ya yi da dukkan masu mukaman na gwamnatin a cikin gidan gwamnatin a daren ranar Talata.

Shugaba Buhari zai kai ziyara Jihar Zamfara ranar Alhamis
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce Buhari zai ziyarci jiharsa a ranar Alhamis. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Buhari: Ka da 'Yan Najeriya su cire tsammani daga Super Eagles

Gwamnan ya ce shugaban kasar zai kai ziyara jihar ne don yi wa mutanen karamar hukumar Anka da na Bukkuyum jaje akan hare-haren da aka kai musu inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Gwamnan ya bukaci kowa ya kiyaye dokoki

Matawalle ya ce:

“An shirya komai musamman don tarbar shugaban kasar yadda ya dace.
“Ina so in sanar da mutanen Jihar Zamfara cewa shugaban kasar Najeriya zai kawo ziyara ranar Alhamis musamman don yi wa mutanen Anka da Bukkuyum jaje akan hare-haren da aka kai musu.”

Gwamnan ya bukaci duk mazaunan Jihar su kasance masu bin dokoki yayin da shugaban kasar ya kai ziyara.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa zan nemi takarar kujerar Buhari a 2023 – Tsohon gwamnan Zamfara

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164