Ka dau shawarata kawai, ka daina kame-kame: Gwamna Ortom ya yiwa Buhari raddi
- Gwamnan jihar Benue ya mayarwa fadar shugaban kasa martani bisa jawabin da Malam Garba Shehu yayi
- Mai magana da yawun Ortom yace rashin hankali ne maganar Garba Shehu cewa Ortom na daukan nauyin yan bindiga
- Ortom yace shekara guda kenan yana neman ganawa da Shugaba Buhari amma an yi masa katanga
Makurdi - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi kira ga fadar shugaban kasa ta daina kame-kame, kawai ta mayar da hankali kan abubuwan da ke damun Najeriya.
Ortom ya bayyana hakan ne a martanin da yayi kan jawabin da kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yayi a hirarsa da tashar AriseTV.
Sakataren yada labaran gwamnan, Nathaniel Ikyur, ya saki martanin Ortom a jawabin da ya saki ranar Laraba, rahoton TheCable.
Yace maimakon magana kan matsalolin da Najeriya ke fama da su, gwamnatin Buhari tana kokarin suka da batawa Ortom suna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, abin takaici ne gwamnatin Buhari da ta dade tana sukar gwamnatocin baya na tuhumar Ortom don ya soki gwamnatocin da suka gabaceshi.
Yace:
"Tsawon shekara guda, an hana Gwamnan ganin shugaban kasa, wannan ma karya ne?"
"Shin gwamnatin Buhari bata kashe biliyoyin daloli kan gyaran matatun man fetur ba amma har yanzu babu amfani? Shin Gwamna Ortom ne ya hana shugaban kasa gyaransu? Me ya hana Garba Shehu ambaton maka amma ya sharesu."
"Maimakon haka, yayi ta kame-kame yana kokarin batawa gwamnan suna. Ya tuhumi gwamnan da daukar nauyin yan bindiga. Wannan rashin hankali ne."
Fadar shugaban kasa ta fito, ta caccaki Gwamna Samuel Ortom
Fadar shugaban kasa ta dura kan gwamnan Benuwai a dalilin fitowa da ya yi a wani gidan talabijin, ya na mai sukar Mai girma Muhammadu Buhari.
Malam Garba Shehu ya fitar da wani jawabi na musamman wanda ya yi wa take "The Incongruence of Governor Samuel Ortom on Arise TV” a yammacin jiya.
Hadimin shugaban kasar ya ce Ortom yana yawan daura laifi kan Muhammadu Buhari wanda duk da halin da ake ciki, yana biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya.
A cewar Garba Shehu, a maimakon gwamnan ya biya ma’aikatansa albashi, yana sukar Buhari. Abin na sa har ma ya kai yana cin mutuncin wadanda yake mulka.
Asali: Legit.ng