Nasrun Minallah: Gwarazan Sojoji sun halaka dandazon mayakan ISWAP, sun tarwatsa sansanin su a Neja

Nasrun Minallah: Gwarazan Sojoji sun halaka dandazon mayakan ISWAP, sun tarwatsa sansanin su a Neja

  • Gwarazan sojojin Najeriya sun samu nasarar tarwatsa tawagar yan ta'addan ISWAP dake kokarin kafa sansani a Kaiji Park
  • Kwamishinan tsaro a jihar Neja ya tabbatar da cewa dandazon yan ta'adda sun mutu, yayin da sojojin suka kame wasu da dama
  • Yace an jawo hankalin gwamnati kan yan ta'addan dake shigowa sassan jihar musamman yankunan dake da albarkatun noma

Niger - Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayaƙan ISWAP da dama, kuma sun ragargaza sansanin su daga Kainji National Park, ƙaramar hukumar Birgu a jihar Neja.

Daily Trust ta rahoto cewa Kwamishinan kananan hukumomi da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata a Minna.

Yace ya zama wajibi sojojin su ɗauki mataki kan yan ta'addan kasancewar sun fara yunkurin mayar da filin Kainji National Park wani sansanin su.

Kara karanta wannan

Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

Sojojin Najeriya
Nasrun Minallah: Gwarazan Sojoji sun halaka dandanzon mayakan ISWAP, sun tarwatsa sansanin su a Neja Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan dake tsero wa daga luguden wutan sojoji a jihohin dake makwaftaka da Neja, sun fara kafa sansanoni a cikin jihar Neja.

Kwamishinan ya ce:

"Mafi yawan yan ta'addan sun sheƙa lahira, yayin da jami'an sojin suka damƙe adadi mai yawa. Yanzu haka ana tsare da su a magarkamar yan sanda."

Wane mataki gwamnatin Neja ke ɗauka?

Umar ya ƙara da cewa an jawo hankalin gwamnati kan yan ta'adda da dama sun shigo jihar musamman a yankunan da ake kiwon dabbobi da kuma ƙasar noma.

Sai dai ya tabbatar da cewa gwamnatin Neja ta tashi tsaye domin yaƙar su da kuma kare rayukan al'umma da dukiyoyin su.

"Mun matsa ƙaimi sosai domin tabbatar da cewa yan bindiga ba su sake koma wa waɗan nan yankuna ba."

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bindige 'yan sanda har Lahira, sun yi awon gaba da babban ɗan kasuwa a Jigawa

A wani labarin na daban kuma Magidanci ya lakaɗawa budurwarsa dukan kawo wuƙa, ya shaƙe ta har ta mutu

Hukumar yan sanda reshen jihar Ondo na cigaba da bincike kan wani magidanci ɗan shekara 40, Olasunkami Oluwole, bisa zargin shaƙe budurwarsa har ta mutu.

Iyalan mamaciyar sun bayyana cewa mutumin ne ya gayyaci yar uwarsu, kuma suna zargin cewa shi ne ya kashe ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262