Zamfara: An gurfanar da dillalin motocci kan zargin cin 'sassan jikin yaro' dan shekara 9
- A ranar Talata wani fitaccen dilan motoci da ke Gusau, Jihar Zamfara da wasu mutane 4 suka gurfana gaban kotun majistare bisa zargin su da halaka yaro dan shekara 9
- Mahaifiyar yaron, Jamila Abdurrahman Hafiz ta roki kotu inda ta bukaci kotu ta bi mata hakkin dan ta saboda bai ji ba bai gani ba suka halaka shi
- Hakan yasa alkalin duk da dage karar zuwa ranar 7 ga watan Fabrairun 2022 da ya yi ya bukaci a garkame duk wadanda ake zargin cikin gidan gyaran hali
Jihar Zamfara - Wani fitaccen dilan motoci tare da wasu mutane hudu a Gusau, babban birnin jihar Zamfara sun gurfana gaban wata kotun majistare ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.
Hakan ya biyo bayan zargin su da ake yi da halaka yaro mai shekaru 9, Ahmad Yakubu Aliyu tare da cin naman sa.
Jami’an tsaro suka gabatar da wadanda ake zargin gaban kotu.
Duk sun musanta zargin da ake musu
Mai gabatar da kara, Sa’adu Gurbin Bore, ya karanto duk laifukan da ake zargin su da aikatawa inda duk suka musanta a gaban kotu.
Daga nan alkalin ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Fabrairun 2022.
Tun farko iyaye da sauran jama’an gari sun shiga cikin kotun suna bukatar a yi adalci ga dan su da aka halaka.
Sun ce sun shiga tashin hankali bayan kisan yaron kuma ba za su taba yafe wa wadanda suka aikata mummunan laifin ba.
Alkalin ya bukaci a sakaya wadanda ake zargin a gidan gyran hali
Mahaifiyar yaron, Jamila Abdurrahman Hafiz, ta sanar da Daily Trust cewa sun je kotun ne don tabbatar da an yi adalci ga yaronta da aka halaka ba tare da ya ji ko ya gani ba.
Alkalin ya bukaci a wuce da wadanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali da ke Gusau don a adana su.
An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona
A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.
Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.
Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.
Tsokacin Edita: Da farko mun ari hoton Daily Trust wanda ke nuna mahaifin wanda abin ya afkawa maimakon wanda kae tuhuma da laifin. Mun yi nadamar hakan kuma muna neman afuwa. Yanzu mun sauya.
Asali: Legit.ng