Daga karshe: Gwamnatin Kwara ta amince mata musulmai suke sanya hijabi a makarantu
- Bayan da aka samu rikice-rikice kan lamuran da suka shafi addini a jihar Kwara, gwamnati ta fitar da mafita
- Gwamnati ta amince da mata musulmai su sanya hijabi a makarantun gwamnati na fadin jihar ta Kwara
- An kuma bukaci makarantun gwamnati da su dauki umarnin, sannan su tabbatar da fara bin dokar da aka sa
Jihar Kwara - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kwara ta ce ‘yan mata musulmi da ke son shiga makarantun gwamnati a yanzu suna da ‘yancin sanya Hijabi a makaranta.
Kwamishiniyar ilimi ta jihar Hajia Sa’adatu Modibbo Kawu ce ta bayyana hakan a lokacin wani taron zaman lafiya da masu ruwa da tsaki na musulmi da kirista a garin Ijagbo dake karamar hukumar Oyun ta jihar.
A cewar kwamishinar:
Kada dai a samu hanyar tatsar masu makarantun kudi: PDP ta gargadi Ganduje kan batun lasisin makarantun kudi
“Bayanin manufofin gwamnatin jihar Kwara na ba wa ‘yan mata musulmai damar sanya hijabi a duk makarantun gwamnati, ciki har da wadanda ake ba tallafin karatu. Wannan ya yi daidai da hukunce-hukuncen shari’a na kotunan shari’a da kuma kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.”
Don haka ta yi kira ga shugabannin Musulmi da Kirista da su bari a samu zaman lafiya a jihar.
Hajiya Modibbo-Kawu ta kuma umurci shugaban makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo da ta gaggauta aiwatar da sanarwar manufofin gwamnati kan sanya hijabi da aka amince da su a makarantun gwamnati.
Ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana kokarin kawo cikas ga zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar zai fuskanci fushin doka, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Taron ya samu halartar sakatariyar dindindin, Misis Mary Adeosun; shugaban hukumar aikin koyarwa, Alhaji Taoheed Bello da shugabannin hukumar kula da ayyukan koyarwa.
Hakazalika, shugaban kungiyar shugabannin makarantun sakandire ta Najeriya (ANCOPSS), Alhaji Toyin Abdullahi da shugaban kungiyar malamai ta Najeriya (NUT), Alh Umar Abdullahi duk sun hallara
A bangaren taron an samu halartar shugabannin addinai na kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen Ijagbo, Rabaran Samuel Ajayi da shugaban masu ruwa da tsaki na musulmin Offa/Oyun, Alh Abubakar AbdulWasiu da dai sauransu.
Hana dalibai sanya hijabi a Boko: Gwamnan jihar Kwara ya kulle makarantu 10
A wani labarin a can baya, gwamnatin jihar Kwara a ranar Juma'a ta bada umurnin kulle wasu makarantu mallakin coci a Ilori har sai an kammala tattaunawa kan lamarin hana dalibai sanya hijabi a makarantun.
Daily Trust ta ruwaito cewa Sakatariyar din-din-din na ma'aikatar ilimin jihar, Kemi Adeosun, ta saki jawabin cewa makarantun da hakan ya shafa sun hada da Cherubim and Seraphim (C&S) College, Sabo Okea d St.
Anthony College, Offa Road. Sauran sune ECWA School, Oja Iya, Surulere Baptist Secondary School da Bishop Smith Secondary School, Agba Dam.
Asali: Legit.ng