Ustazai: Wankan kamala na amarya da ango a wajen liyafar aurensu ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta
- Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar hoton wasu ustazai a wajen liyafar aurensu
- A cikin hoton an gano amaryar ta yi shiga ta kamala harda doguwar hijabinta har kasa da safar kafa inda shi kuma ango ya sanya babbar riga da hula
- Wannan shiga da amaryar ta yi shi ne ya fi daukar hankalin jama'a inda da yawa suka yaba mata, wasu kuma na ganin shi kanshi liyafar bai dace ba
Kamar yadda yake a wannan zamani, kowace budurwa kan so ta yi bikin aure cikin ado na kece raini musamman yanzu da ake Allah-Allah a watsa hotunan ma'aurata a shafukan soshiyal midiya.
Wannan ya sa mutane da dama sun yi watsi da al'adarsu tare da aron na wasu su yafa. Misali a zamanin baya a arewa da wuya ka ga amarya ta yi shiga ta nuna tsaraici da sunan ado, amma a yanzu hakan ya zama gama-gari duk da sunan wayewa da son nuna isa da burgewa.
Sai dai wata amarya da aka yi kwanan nan ta sauya tsarin, inda ta tabbatar da cewa ana iya yin duk wani liyafa ba tare da an zub da kamala da nutsuwa ba.
A cikin wani hoto da ya bayyana a shafukan soshiyal midiya, an gano amaryar tare da angonta cikin shiga ta kamala a wajen liyafar bikinsu.
Amaryar dai ta sanya doguwar hijabinta har kasa da safar kafa tare da yar karamar jakarta a hannu sannan ta sha lallenta, inda shi kuma angon ya sanya babbar riga da hula.
Wannan shiga ta amaryar ya dauki hankalin jama'a sosai inda da dama suka jinjina mata kan wannan mataki da ta dauka na kare mutuncinta. Sai dai wasu na ganin shi kanshi liyafar wani bidi’a ne.
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin da mabiyanta na Facebook suka yi
Bashir Idris Mlf ya yi martani:
"Sun fito daga gida mai daraja ne shiya sa"
Fatima Xahrah Shi'ite ta ce:
"Haka Yakamata Kowacce 'Yar Musulmai Takasance Lokacin Shagalin Bikinta Domin Kare Dokokin Ubangiji Da Neman Albarkar Aure.
"Ba Lokacin Aure Kadai Bama A Kowanne Yanayi Haka Yakamata Mace Musulma Ta Zama Cikin Suturce Jikinta."
Al Hamzat Shoe ya rubuta:
"Kuma da alama yarabawa ne kaga abin kunya ne agun wasu hausawan wai Mace sai ta nuna tsaraici awajen bikinta shine ta burge Allah yabasu zaman lafiya."
Ari Kimé Maïna ya ce:
"Masha'allah Haka yana nuna ta san komine zaman aure."
Deenee Yahaya ya yi martani:
"To dinar dole ce inso suke su nuna su na Allah ne ai bama zasu yrd suyi dinner ba"
Ibrahim Fika ya ce:
"Sabon salon yaudara da rikitar da hankalin jama'a abi dokokin Allah wajen gudanarda shagulgulan aure itache mafita"
Muslima Bintoul Islam ta ce:
"Anyi ba'ayi ba. A sabawa Allah ma harda wani basaja, nina dauka ma walima ne fa , sai kace dole sai anyi abinda Allah ya haramta. Allah ya qara shiryar damu hanya madaidaiciya."
Ni na yi mata komai: Saurayin da budurwarsa ta ki amincewa ta aure shi ya magantu cikin hawaye
A gefe guda, mutumin da budurwa ta tozarta a yayin da ya nemi ta aure shi ya bayyana wasu sirrika game da soyayyar tasu wacce ta yi tsami a yanzu.
Bayan rashin nasara a bukatar auren, mutumin wanda yake mazaunin Abuja ya haifar da yar dirama a wajen wani bikin zagayowar ranar haihuwa wanda a nan ne ya ga budurwar tare da sabon saurayinta.
A wani sabon bidiyo inda a ciki yake bayanin dalilinsa na aikata abun da ya yi, mai gyaran wayoyin ya bayyana cewa ya shafe tsawon shekaru hudu yana soyayya da budurwar.
Asali: Legit.ng