Dan Allah ku taya ni da addu’ar samun lafiya, Olisa Metuh ya roki ‘yan Najeriya

Dan Allah ku taya ni da addu’ar samun lafiya, Olisa Metuh ya roki ‘yan Najeriya

  • A cikin wani yanayi na ban tausayi da radadin ciwo, tsohon kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Olisa Metuh, ya roki yan Najeriya da su taya shi da addu'a
  • Metuh ya yi wannan roko ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 21 ga watan Janairu, inda aka gano shi kwance a gadon jinya
  • Ya ce an yi masa tiyata da yawa a shekarar da ta gabata amma kuma a yanzu ya samu wani labari mai ban tsoro daga likitocinsa

Tsohon babban sakataren labarai na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Olisa Metuh, ya yi kira ga yan Najeriya da su taya shi da addu'a kan yanayin da lafiyarsa ke ciki.

Metuh, a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, ya ce an yi masa tiyata da dama a cikin shekarar da ta gabata, inda ya kuma saka hotonsa a kan gadon asibiti.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ga yan Najeriya: Ba zan ci amanarku ba idan kuka zabe ni shugaban kasa a 2023

Dan Allah ku taya ni da addu’ar samun lafiya, Olisa Metuh ya roki ‘yan Najeriya
Dan Allah ku taya ni da addu’ar samun lafiya, Olisa Metuh ya roki ‘yan Najeriya Hoto: Olisa Metuh
Asali: Facebook

Metuh ya rubuta a shafin nasa:

"Cikin shekara daya da ta gabata, an yi mani aikin tiyata da dama kuma na yi imani da Allah wannan zai zama na karshe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Komai fushin da kuke yi dani da maganata ko kalubalen da ya shafi mulki a wancan lokacin, don Allah ku yi mani addu'a.
"Yanayin lafiyata ta tabarbare sosai, ba abu ne mai sauki ba kuma rahamar Allah ce kadai ke dawainiya da ni.
"Na samu wasu labarai masu ban tsoro daga likitocin a yau amma ina ci gaba da kadaita Allah kuma da addu'o'inku da Ikon sa na warke kuma zan kasance cikakke da izinin sunan Yesu."

Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Olisah Metuh, ta bukaci sake shari'a

A wani labarin, mun ji a baya cewa kotun daukaka kara dake zama a Abuja ta rushe hukuncin da aka yanke wa Olisa Metuh, tsohon kakakin jam'iyyar PDP, shekaru 7 a gidan gyarann hali, The Cable ta wallafa hakan.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

A ranar Alhamis, an zargi alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Okon Abang, yayi rashin adalci wurin yankewa tsohon kakakin jam'iyyar PDP hukunci.

Okong Abanga ya yanke wa Metuh hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng