Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Olisah Metuh, ta bukaci sake shari'a

Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Olisah Metuh, ta bukaci sake shari'a

- Kotun daukaka kara ta rushe hukuncin da babbar kotun tarayya ta yankewa Olisa Metuh

- Ana zargi alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Okon Abang, da yanke masa hukunci bisa rashin adalci ne

- Alkalin ya yankewa tsohon kakakin jam'iyyar PDP din shekaru 7 a gidan gyaran hali, shine ya daukaka kara

Kotun daukaka kara dake zama a Abuja ta rushe hukuncin da aka yanke wa Olisa Metuh, tsohon kakakin jam'iyyar APC, shekaru 7 a gidan gyarann hali, The Cable ta wallafa hakan.

A ranar Alhamis, an zargi alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Okon Abang, yayi rashin adalci wurin yankewa tsohon kakakin jam'iyyar PDP hukunci.

Okong Abanga ya yanke wa Metuh hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.

EFCC ta zargi Metuh da satar N400,000,000 a lokacin yana rike da matsayin mai bayar da shawara na musamman a harkar tsaro ga gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Tsoffin sanatoci da 'yan majalisu suna zawarcin Tinubu don shugabanci kasa a 2023

Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Olisah Metuh, ta buakci sake shari'a
Kotun daukaka kara ta soke hukuncin Olisah Metuh, ta buakci sake shari'a. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

A ranar 25 ga watan Fabrairun 2020, kotun ta yanke masa hukuncin yin shekaru 7 a gidan gyaran hali bayan ta gamsu da satar duk kudaden da ake zarginsa dashi.

KU KARANTA: Ana tsaka da matsalar tattalin arziki, mazauna Guaca sun samu ziinarai da zurfa a kauye kauyensu

A wani labari na daban, Sanata Rufai Hanga ya yi hasashen dalilin da yasa shugaba Buhari ya ki sauke shugabannin tsaro.

Hanga ne sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar tarayya, ya sanar da Daily Sun dalilin da ya sanya Buhari ya ki sauke shugabannin tsaro. Mutane da dama sun yi ta caccakar Buhari saboda kin sauke shugabannin tsaro.

Sanatan ya ce Buhari yana tsoron kananan jami'an tsaron da zai daura a kan mulki ba za su iya mara masa baya kamar wadannan shugabanni ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng