Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori

Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori

  • A jihar Kwara, an hana barace-barace kan titunan babbar birnin Ilori daga yanzu
  • Gwamnatin jihar ta yi yarjejeniya da shugabannin al'ummar Hausawa mazauna jihar Kwara
  • Jihohin Arewacin Najeriya da dama su haramta barace-barace da almajiranci

Gwamnatin jihar Kwara ta haramta baran titi a fadin birnin jihar Ilori, Kwamishanar raya gari, . Abosede Aremu, ta bayyana hakan a zama da masu ruwa da tsaki, rahoton Leadership.

Abosede tace gwamnatin jihar ta dau wannan mataki ne don dubi ga irin illolin da barace-barace ke haifarwa a manyan titunan jihar.

Kwamishanar tace ma'aikatarta da al'ummar Hausawan Ilori sun rattafa hannu kan takardar yarjejeniya kan lamarin.

Ta jaddada irin ukubar da za'a yiwa duk wanda aka kama yana bara a titi na tara ko dauri a gidan yari bisa ga dokar hana bara ta 2006.

Kara karanta wannan

A yanzu haka: Mayakan Boko Haram sun shiga Chibok, su na luguden wuta

Wakilan al'ummar Hausawa, Surajudeen Hussain, Rufai Sanni da Mohammed Lawal, sun tabbatarwa gwamnatin jihar cewa zasu bada hadin kai wajen tabbatar da dabbaka wannan doka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori
Gwamnatin Kwara ta haramta bara a jihar, ta yi yarjejeniyar da al'ummar Hausawar Ilori

Gwamna Ya Ba da Umarnin a Kwashe Mabarata Zuwa Wurin Alfarma a Jiharsa

A Oyo kuwa, tuni Gwamnatin jihar ta fara aikin kwashe mabarata daga lungunan Jemibewon, yankin Mokola-Sabo na Ibadan zuwa sabuwar cibiyar sake matsuguni na Akinyele da aka gina a cikin garin.

Wakilin Legit.ng da ke Ibadan, Ridwan Kolawole, ya ruwaito cewa cibiyar sake matsugunin da ta fara watannin baya, an bude ta ne da sanyin safiyar Talata, 15 ga Yuni, 2021

Wannan ya biyo bayan rangadin sabon wajen ne da shugabannin al’ummar Arewa da wakilan mabaratan suka yi a ranar Asabar, 12 ga Yuni.

Kara karanta wannan

Idan kuka kara farashin mai, zaku sake jefa miliyoyin mutane talauci: Janar AbdulSalam

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: