Kotu ta sake mai garkuwa da mutane kan hujjan yana da tabin hankali lokacin da ya aikata laifin

Kotu ta sake mai garkuwa da mutane kan hujjan yana da tabin hankali lokacin da ya aikata laifin

  • Ma'aikatar shari'ar jihar Jigawa ta bayyana yadda kotu ta saki wani mutumin da yayi garkuwa da yaron makwabta
  • Kotu ta wanke mutumin ne bayan Likitoci sun bayyana cewa yana fama da cutar tabin hankali
  • Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan hukunci da kotu ta yanke a jihar Jigawa

Kazaure - Wani mutumi da aka kama da laifin sace dan shekara shida ya samu yanci bayan kotu ta gano cewa yana da tabin hankali lokacin da ya aika laifin.

Mai magana da yawun ma'aikatar shari'ar jihar Jigawa, Zainab Baba-Santali, ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Juma'a, rahoton Premium Times.

mai garkuwa da mutane na da tabin hankali
Kotu ta sake mai garkuwa da mutane kan hujjan yana da tabin hankali lokacin da ya aikata laifin HOtu: Kotu
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jami'ai sun kyauta: Buhari ya yi martani kan kame mai malamin da ya sace Hanifa

An damke mai garkuwa da mutanen mai suna Safiyanu Rabiu da laifin rabawa yaran makwabta alewa sannan ya sace daya cikinsu.

Sai ya kai yaron wajen yayar mahaifiyarsa inda yace mata iyayen yaron sun yi tafiya.

Daga baya ya kira wani makwabci don ya fadawa iyayen yaron cewa an sace yaronsu. Hakazalika ya bukaci kudin fansan milyan daya ko a kashe yaron, tace.

Tace:

"Daga baya aka kamashi kuma ya amsa laifin cewa ya aikata hakan. Amma lauyan mutumin ya kira shaidu uku, ciki har da Likita daga asibitin mahaukatan Kazaure kuma suka gabatar da hujja."
"Kotu ta yanke hukuncin cewa duk da lauyoyin gwamnati sun fadi gaskiya, mutumin da ya aikata laifin ya gabatar da hujjar cewa lokacin da ya aikata laifin yana fama da tabin hankali. Saboda haka kotu ta wanke shi kuma tace a sake shi."

Ga jawabin yan Najeriya:

Aliyupakee Abubakar:

Uhhmm..Nigeria kenan yana da iyayen gida a gwamnati dole yasamu tabin hankali..

Kara karanta wannan

Na yi tawakkali ga Allah, amma ba zan taba mantawa ba: Mahaifin Hanifa ya magantu

Allah ya isa kuma Allah yakawo mana me kishinmu

Rabiu Adamu:

Allah ya kawomana karshe matsiyata azzalumai fir'auna ma yagama zalunchin shi yamutu sakkontana ma'aikatan kotu Kuma ku shirya gamuwanku da Allah.

Sani Yusuf:

Kai jama'a wata shari'a sai akasata Nigeria, wai mahaukaci yayi garkuwa da Mai hankali Kuma ankaishi kotu alkali ya sallameshi Yana da tabin hankali, wallahi duk shari'ar da akayi bisa son rai! Allah Yana nai amadakata, a inda babu lauya. Sannan jama'a ku Kula da mahaukacinnan saboda an riga an sallameshi.

Mudassir Jaafar:

Taf Lallai kuma har yasan yayi garkuwa da mutane ya nemi fansa. Shima kau alkalin Kotun ya kamata a koreshi aiki saboda yana da tabin hankali

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng