AFCON: Matasa sun dira gidan dan kwallon da ya zubar da fenariti a wasar Sierra Leone da Guinea

AFCON: Matasa sun dira gidan dan kwallon da ya zubar da fenariti a wasar Sierra Leone da Guinea

  • An ji waje da kasar Sierra Leone daga gasar kofin nahiyar Afrika bayan shan kashi hannun Equitorial Guinea
  • Wannan fadi da Sierra Leaone tayi ya bar baya da kura yayinda matasa suka kai farmaki gidan daya daga cikin yan kwallon
  • Hakan ya biyo bayan zubar fenaritin da yayi ana saura minti biyar a tashi wasa

Jami'an yan sanda sun hana fusatattun masoya kona gidan dan kwallon Sierra Leone, Kei Kamara, a birnin Freetown bayan zubar da fenariti da ya sabbaba fitarsu daga gasar AFCON 2021.

A daren Alhamis, Sierra Leone ta sha kashi hannun Equatorial Guinea da ci daya mai ban haushi a wasarsu ta karshe.

Ana kasa da minti goma a tashi wasa, Sierra Leone ta samu fenariti bayan Issa Kallon ya kifar da Ganet cikin akwatin 18, rahoton Complete Sports.

Kara karanta wannan

Bayan an yi waje da zakarun 2019, Super Eagles sun san da wa za su hadu a AFCON

Kamara ya haye kan kwallon domin buge fenaritin amma mai tsaron gidan Equatorial Guinea, Jesus Owono, ya bugeta.

Sierra Leone da Guinea
AFCON: Matasa sun dira gidan dan kwallon da ya zubar da fenariti a wasar Sierra Leone da Guinea Hoto: Complete Sports
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya samu nasarar jefa kwallon raga, da Sierra Leone ta haye zagaye na biyu matsayin daya daga cikin kasashen na suka zo na uku amma suka fi kokari.

Sakamakon haka, an tattaro cewa matasa sun taru a gidan Kei Kamara domin yi masa barna amma jami'an tsaro suka hanasu.

Equatorial Guinea yanzu ya haye tare da kasar Côte d’Ivoir.

AFCON 21: ‘Yan wasan Najeriya za su gwabza da kasar Tunisiya a zagaye na gaba

Yan wasan Super Eagles na Najeriya za su goge raini da kasar Tunisiya a zagaye na biyu na gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afrika.

Rahotanni sun tabbatar da Najeriya za ta hadu da Tunisiya bayan kasar Arewacin Afrikar ta samu fitowa daga gurbin rukuni, bayan an yi waje da Aljeriya.

Kara karanta wannan

A yanzu haka: Mayakan Boko Haram sun shiga Chibok, su na luguden wuta

Zakarun nahiyar Turai na 2019, Aljeriya sun sha kashi a wasansu na karshe a hannun Ivory Coast da ci 1-3. Haka zalika Gimbia ta doke Tunisiya da ci 1-0.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng