Kisan gillar Hanifa: Gwamna Ganduje ya magantu, ya bayyana matakin da za a dauka

Kisan gillar Hanifa: Gwamna Ganduje ya magantu, ya bayyana matakin da za a dauka

  • Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya sha alwashin tabbatar da adalci a batun yin garkuwa da Hanifa Abubakar da kuma kashe ta
  • Kun ji cewa masu garkuwa da Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar sun kashe ta duk da karbar kudin fansa daga hannun iyayenta
  • Ya ce gwamnati ta damu matuka yadda mutanen da aka damka wa kulawar yara suka rikide suka zama masu kashe su

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da tabbacin cewa gwamnati za ta ci gaba da sanya ido sosai tare da tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da laifi a yin garkuwa da kisan gilla da aka yi wa Hanifa Abubakar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Malam Muhammad Garba ya fitar.

Kara karanta wannan

Babbar magan: Gwamna ya sanya hannu ya doka mai tsauri ta hana kiwo a fili

Gwamnan ya ce tuni matakan da aka dauka a lamarin sun fara aiki, ciki har da rufewa da kuma janye lasisin gudanar da makarantar ba tare da bata lokaci ba.

Gwamna Ganduje ya magantu kan lamarin Hanifa
Kisan gillar Hanifa: Gwamna Ganduje ya magantu, ya bayyana matakin da za a dauka | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Depositphotos

Ya ce gwamnati ta damu matuka yadda mutanen da aka damka wa amana da kulawar yara suka rikide suka zama masu kashe su da wulakanta gawarwakinsu.

Ganduje ya kara da cewa gwamnati na tuntubar iyayen yarinyar inda za ta ci gaba da alaka dasu har sai an tabbatar da adalci a batun don ya zama izina ga wasu.

Gwamnan wanda ya yabawa jami’an tsaro a jihar kan daukar matakan da suka kai ga cafke wadanda ake zargi da hannu a lamarin, ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, gwamnati za ta bi diddigin lamarin har ta kai ga gaci.

Kara karanta wannan

Almundahanar N29bn: Kotu ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan Adamawa da dansa kan dakatar da kara

Ya kuma yabawa kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil-adama da kuma ‘yan Najeriya masu kishin kasa da suka damu da lamarin.

Ganduje ya kuma ba da tabbacin goyon bayan hukumomin tsaro na gwamnati wajen gudanar da ayyukansu na ganin cewa Kano ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

A bangare guda, shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School, Kawana, Kano, Abdulmalik Tanko, ya bayyana yadda ya yi amfani da gubar bera na Naira 100 wajen kashe daya daga cikin dalibansa.

A baya an ruwaito yadda wasu miyagu suka yi garkuwa da Hanifa Abubakar, ‘yar shekaru biyar yayin da take kan hanyarta ta dawowa daga makarantar Islamiyya a watan Disamba kuma suka yi mata kisan gilla.

Tanko dai ya bukaci iyayen yarinyar da su biya kudin fansa Naira miliyan 6 amma ya shiga hannu yayin da yake kokarin karbar kudin fansan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin da yasa Gwamnatin Tarayya ba za ta dena karɓo rancen kuɗi ba, Lawan

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.