Borno: Ɗalibin sakandare ya keta makogwaron ɗalibin ƙaramin aji da reza don ya sa shi aiki ya ƙi yi

Borno: Ɗalibin sakandare ya keta makogwaron ɗalibin ƙaramin aji da reza don ya sa shi aiki ya ƙi yi

  • Umar Goni, dalibin aji 5 na sakandare yana hannun rundunar ‘yan sandan jihar Borno bisa yunkurin halaka wani dan uwansa dalibi da ya yi
  • Hakan ya auku ne bayan ya yi amfani da reza wurin yanke wuyan Jibrin Sadi Ramadan, dalibin da ke kasa da ajin su bayan wani kankanin rikici
  • An samu bayanai dalla-dalla akan yadda lamarin ya auku a wata makaranta mai zaman kanta ta musulmai, Kwalejin El-Kanmi da ke Maiduguri ranar Laraba

Borno - Umar Goni, dalibin da ke babbar aji a makarantar su yana hannun jami’an rundunar ‘yan sanda bayan yunkurin halaka wani dalibin na karamin aji da ya yi a makarantar su, Daily Trust ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda ya yi amfani da reza wurin yankar makogwaron Jibrin Sadi Ramadan, daya daga cikin daliban kananun aji, bayan wani karamin rikici ya shiga tsakanin su.

Kara karanta wannan

Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga

Borno: Ɗalibin sakandare ya keta makogwaron ɗalibin ƙaramin aji da reza don ya sa shi aiki ya ƙi yi
'Dalibin sakandare ya keta makogwaron ɗalibin ƙaramin aji da reza don ya sa shi aiki ya ƙi yi a Borno. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wakilin Daily Trust ya tattaro bayanai akan yadda lamarin ya faru a bayan dakunan kwanan daliban da ke Kwalejin El-Kanemi mai zaman kanta da ke Maiduguri cikin Jihar Borno, ranar Laraba da dare.

Majiya ta bayyana yadda Goni ya aiki Ramadan, wanda bai wuci shekaru 12 ba, sai ya ki zuwa, hakan yasa ya janyo Ramadan zuwa wurin da babu mutane ya yanki wuyansa da reza sosai.

An tsinci Ramadan kwance a cikin jini

Majiyar ta shaida yadda aka tsinci Ramadan kwance cikin jini a can bayan dakunan kwanan dalibai.

Daga bisani aka wuce da shi asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri inda aka kwantar da shi ana kulawa da lafiyarsa.

Yanzu haka Ramadan na bangaren ICU ana kokarin ceto shi don yana kwance ne rai a hannun Allah kamar yadda majiyar ta shaida.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya mutu yayinda yake kokarin satar wayoyin Taransfoma

Wani ma’aikacin makarantar ya kwatanta lamarin da mummunan aiki, inda ya koka akan halayyar wasu malaman makarantar kwana ga yaran masu kudi.

Ya ce ana nuna fifiko ga yaran masu hannu da shuni

Ya zargi lamarin da samun nasaba da yadda malamai suke nuna fifiko ga wasu dalibai duk don samun abin duniya daga hannun iyayen su.

Wanda ake zargin yana bangaren binciken sirri na musamman inda ake tuhumar sa da yunkurin yin kisan kai.

A wata tattaunawa da Daily Trust ta yi da Nasiru Mato, kawun wanda mummunan lamarin ya auku da shi ya ce sun gano yadda babban dalibin wanda aka fi sani da Fairoz ya janye karamin dalibin zuwa bayan dakuna ya yi amfani da reza wurin yankar wuyansu ta wurare daban-daban.

Ya yanki wasu jijiyoyin wuyansa

A cewarsa:

“Sai da dan mu ya suma bayan wanda ya yi masa aika-aikan ya tsere yana tunanin ya halaka shi. Mun samu kira na gaggawa daga hukumar makarantar da safiyar Laraba wanda aka zarce da shi asibitin koyarwa na Maiduguri a mawuyacin yanayi.

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

“Yanzu haka ya yayyaki wasu jijiyoyin wuyansa. Kuma muna bukatar a bashi kula ta musamman a asibitin. An ci gaba da bincike kuma an kama mai makarantar.”

Mato ya ce iyayen yaron ba su gamsu da yadda hukumar makarantar ta dauki matsalar ba, kamar babu wani kula.

Ya kara da cewa yanzu haka da wanda ya yi aika-aikar ya ke hannun ‘yan sanda, ya ki fadada bayani akan kansa.

Wata majiya daga ‘yan uwan yaron, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce hukumar makarantar ta gamsar da mijin mahaifiyar yaron da ya yi aika-aikan wanda makusancin makarantar ne akan kada ya daga maganar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164