Ci gaba: Gwamnatin Buhari za ta gina layin dogo daga Minna zuwa tashar jiragen ruwa ta Baro a Neja
- Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta sake gina karamin layin dogo daga garin Minna, babbar birnin jihar Neja zuwa tashar jiragen ruwa ta Baro
- FG ta ce ta dauki wannan mataki ne domin bunkasa harkokin tattalin arziki a jihar ta Neja da jihohin da ke makwabtaka
- Tuni ta amince da bayar da kwangilar sake gina shi a zaman majalisar zartarwa da aka yi a yau Laraba, 19 ga watan Janairu
Neja - Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na sake gina wani karamin layin dogo daga garin Minna, babbar birnin jihar Neja zuwa tashar jiragen ruwa ta Baro.
Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne domin bunkasa harkokin tattalin arziki a jihar ta Neja da jihohin da ke makwabtaka.
Mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmed ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.
Ya kuma bayyana cewar an amince da bayar da kwangilar aikin sake ginin, a zaman majalisar zartarwa a yau Laraba.
Ahmed ya wallafa a shafin nasa:
"Gwamnatin tarayya za ta sake gina wani dan karamin layin dogo daga Minna zuwa tashar jiragen ruwa ta Baro a jihar Neja domin bunkasa harkokin tattalin arziki a Neja da jihohin makwabta, majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da bayar da kwangilar sake gina shi a yau."
Buhari ga 'yan Najeriya: Ku kara hakuri, saura kiris abinci ya yi araha a Najeriya
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci yan Najeriya da su kara hakuri kan halin da ake ciki a yanzu na tsadar kayan masarufi.
Buhari ya bayyana cewa yawan abincin da ake nomawa a kasar, musamman fadada noman shinkafa da aka yi, zai karyar da farashin kayan abinci, ta yadda kowa zai iya siyansa.
Shugaban kasar ya yi magana ne a bikin kaddamar da shirin dalar shinkafa na Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kungiyar Monoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a babban dakin baje kolin kasuwancin kasa da kasa na Abuja, rahoton Leadership.
Asali: Legit.ng